Shinkafi ya ci amanar APC a Zamfara – Yusuf Idris

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar All Progressive Congress APC, reshen jihar Zamfara, ta bayyana Dr. Sani Abdullahi Shinkafi a matsayin mutumi da ke cin amanar jam’iyyar a siyasance a Jihar Zamfara.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Yusuf Idris ya yi wannan furuci a cikin wata sanarwa yayin da yake mayar da martani ga kalaman da Shinkafi ya yi wa shugabannin jam’iyyar kwanan nan.

Jam’iyyar ta bayyana kalaman da Shinkafi ya yi wa shugabannin jam’iyyar kwanan nan, musamman ƙaramin ministan tsaro, Bello Muhammad Matawalle da Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin yunƙurin ɓata sunan su.

Jam’iyyar ta koka da yadda Shinkafi ke yaɗa kalaman da basu dace ba ga Matawalle ta hanyar amfani da yanayin rashin tsaro a jihar don kawai ya ɓata sunan ministan.

“Jam’iyyar tana goyon bayan shugabannin ta biyu, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar da Bello Mohammed Matawalle.”

Yusuf ya bayyana cewa APC har yanzu tana nan a matsayin tsintsiya maɗaurinki ɗaya a jihar ta Zamfara saɓanin rarrabuwar kawuna da Sani Abdullahi Shinkafi yake yayatawa.

“Muna da ƙwarin gwiwa sosai cewa APC na kan hanyar dawowa da ƙarfin ta a Zamfara a 2027 kuma babu wata ɓaraka a tsakanin mambobin jam’iyyar kamar yadda Sani Abdullahi Shinkafi yake yayatawa.” Yusuf ya ce

Jam’iyyar ta yi kira ga Sani Abdullahi Shinkafi da ya guji fakewa da Jam’iyyar PDP mai mulki a jihar don kawo cikas ga zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban APC a jihar.

By ukarofi