Yadda Abdul Maikwashewa ya cika wa Jaruma Halisa Muhammad burinta na ƙarshe

Spread the love

Daga AISHA ASAS

A ’yan kwanakin baya labarin tsohuwar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood Halisa Muhammad, ya kasance ɗaya daga cikin labaran da suka taɓa zukatan mutane, duba da halin da take ciki na rashin lafiyar cutar sanƙar mama, wanda ta fito ta nemi taimakon al’umma don biyan kuɗin magani.

Idan kuna bibiye da mu, kwanaki Manhaja ta ruwaito cewa, wani bawan Allah ya damfareta ya karɓe kuɗaɗen da gwamnan Jihar Kano ya bata don neman lafiyarta, da sunan zai kai ta Saudiya ta ga likitan da zai sada ta da ababen da ake sa ran su zama sanadin waraka gare ta.

A kan hakan Manhaja ta nemi jin ta bakin jarumar, inda ta bayyana mana tiryan-tiryan yadda lamarin ya faru, da kuma halin da ake ciki a lokacin. Ta kuma nemi duk wanda ke iya yin wani abu da ya taimaka ya shiga lamarin don ƙwato mata haƙƙinta daga hannun ɗan damfarar.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, jarumar ta wallafa a shafin ta na Instagram da kuma na Facebook cewa, EFCC sun sanar da ita suna kan bincike wanda zai ɗauki tsayin lokaci. Jarumar ta kuma bayyana wasu maganganu wanda ya shafi burin da take da shi a halin yanzu; 

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Assalamu alaikum. Na samu bayani daga EFCC cewa ana cikin bincike kuma ana ci gaba da gudanar da shi bisa ƙa’ida. Sun shaida min cewa binciken zai ɗauki lokaci, don haka na rungumi haƙuri da tawakkali. Ina roƙon al’umma su ci gaba da yi mana addu’a da fatan alheri abin da ake nufi da haka shikenan kuɗi na ya tafi shi kenan treatment ya kare hasbnallahu wanimal wakil.

“Ni baiwa ce daga cikin bayin Allah da ke fuskantar wata babbar jarabawa ta rashin lafiya – ciwon da ya ɗaure ni, ya raunata jikina, ya girgiza zuciyata. Ga ciwo ga zalunci.

“Ina da buri guda ɗaya kawai a rayuwa: Na je Madina. Na ziyarci fadar Shugaban Halitta, Annabi Muhammad (SAW). Na ga Rawdah mai albarka. Na roƙi Allah da idona cika da hawaye, ga ni a fadar masoyi na annabin rahma sallallahu alaihi wasallam, gida mai tsarki. Na zubar da hawayena a gaban ƙabari mai albarka. Na faɗi damuwata  gani a fadar Allah Mai rahama mai jin kai.

“Wannan shi ne burin da ya rage mini. Burin da nake ganin zai sa ni nutsuwa. Burin da nake ganin zai zama sauyin damuwata da lalurata hakan shi ne waraka ta in shaa Allah.

“Na san akwai waɗanda idan suka ji kuka na, sai zuciyarsu ta karaya. Ina roƙon ku al’umma, ku taimaka min da addu’a da abin da za ku iya, domin cika mun wannan burina. Don Allah ku taimaka min na cimma wannan buri nawa. Na je Madina kafin ƙasa da rufe min ido hawayena ya ƙare.

“A baya ma ku kuka taimaka min  yauma na kawo kuka na  wajen Allah na kawo kuka na wajenku. Ku taimaka min, dan Allah . Ku share min hawaye, Allah zai share naku. Ku sa ni dariya, Allah zai sa ku farin ciki. Allah ya saka muku  da mafificin alkairi Allah ya hana ku ganin irin waɗannan jarrabawar a rayuwarku. Halisa muhammed abdullahi no 0017013473 jaiz bank. 08060819150.”

Wannan rubutu da jarumar mai fama da matsalar kansar mama ta yi, ya janyo hankalin mabiya da masoyanta da dama, wanda da yawa suka taya ta yaɗawa, wasu kuma suka dinga ɗora rubutun nata a nasu shafukan suna taya ta da addu’a.

Za mu iya cewa, addu’ar masoyan jarumar ta samu karɓuwa cikin hanzari, domin jim kaɗan bayan yawaitar tattaunawa kan lamarin burin na Halisa, ta sake wallafa wani rubutun mai ɗauke da hoton shahararren mai shirya fina-finai Abdul Amart Maikwashewa, inda ta yi rubutu kamar haka; “Alhamdulillah. Alhamdullhah. Alhamdullhah. Ina miƙa godiya ta ga Allah Madaukakin Sarki. Me kowa mai komai mai amsar addu’ar bayansa   da ya cika min buri na ta  hannun bawansa Abdul Amart. 

“Ya ce Halisa zo ki tafi madina. Sai na fashe da kuka, don dadi Allah ya faranta maka Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, ya taimake ka a dukkan harkokinka. Allah ya buɗe maka ƙofofin rahama da arziki marasa adadi. Allah ya jiƙan iyayenka, ya kare yaranka, ya albarkaci zuriyarka, ka ci gaba da kasancewa  jagora na alheri a rayuwarmu. Halisa Muhammed.” 

Lamarin ya matuƙar faranta zukatan mutane ta kowane ɓangare, kama daga masoyanta, abokanan sana’arta dama jigo a Masana’antar Kannywood.

Kamar yadda ya wallafa, Editan Blueprint Manhaja, kuma fitaccen marubucin da Kannywood ke alfahari da shi, Nasir S. Gwangwazo, ne ya fara tabbatar da wannan kyauta, inda ya wallafa kafin jarumar ta sanar da labarin.

Gwangwazo ya yi rubuta kamar haka; “Alhamdulillah! Furodusa Abdul Amart ya biya wa Halisa Muhammad kujerar umrah, kamar yadda ta roƙi Allah ya cika mata burin zuwa ziyarar Shugaba (SAW).”

A ɓangare ɗaya kuwa, ƙungiyar masu shirya fina-finai ta ƙasa MOPPAN, ta yaba wa sanannen furodusa a Masana’antar Kannywood, Abdul Amart kan ɗaukar nauyin jaruma Halisa Mohammed zuwa aikin umara.

Sakataren MOPPAN, Dakta Mohd I. Gumel a wata takarda, ya miƙa godiya da jinjina ga furodusan a madadin mambobin ƙungiyar, inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai tausayi da kulawa ga abokan aiki da ma al’umma baki ɗaya.

Ya ce, “wannan taimakon nasa ba shine na farko ba”, abu ne da ya saba yi wa kowane ɗan masana’antar da ke cikin halin buƙatar a tallafa masa.

Sakatare ya ƙara da cewa, “Hakan yasa muke alfahari da kai kuma muke tinƙaho da dukiyar da Allah ya baka. Allah ya saka maka da alkhairansa.

“A ƙarshe, ina maka fatan cin gajiyar wani hadisin Manzon Allah (SAW) da na ji malamai suna hakaitowa cewa, ‘Duk wanda ya zama sanadiyar yaye baƙin cikin bawa a nan duniya, to Allah zai yaye masa bakin ciki ranar tashin kiyama’. Allah ya faranta maka kamar yadda ka farantawa Halisa, kuma mu ma ka faranta mana,” inji Sakataren.

By ukarofi