Kano na shirin karɓar taron fina-finan harsunan asali na Afirka karo na takwas

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Jihar Kano na shirin karɓar baje kolin fina-finai na harsunan asali na Afirka karo na takwas (KILAF), daga ranar 6 zuwa 8 ga watan Nuwamba, 2025. Taken wannan baje koli na bana shi ne “Tsallaka iyakokin ba da labari: Dabarun cimma nasarar harsuna da dama a fina-finan Afirka.”

A wata ganawa da ‘yan jarida a cibiyar NUJ ta Kano, Shugaba kuma Babban Daraktan kamfanin Moving Image Limited, Abdulkareem Muhammad, ya bayyana cewa KILAF ya zama wata babbar kafa wajen tallata labaran Afirka da kuma bambancin al’adunta.

Muhammad ya ce, tun lokacin da aka kafa KILAF a shekarar 2018, ya ɗore a matsayin dandalin nahiyar Afirka da ke ƙarfafa amfani da harsunan gida a fina-finai tare da bunƙasa ƙirƙira a fagen al’adu.

A bana, KILAF ya karɓi fina-finai 616 daga ƙasashe 77, ciki har da fina-finai gajeru, masu tsawo, takardu, fina-finan ɗalibai da kuma na zanen kwaikwayo (animation). Daga cikinsu, 85 daga ƙasashe 30 aka zaɓa don baje koli, inda Najeriya, Masar, Maroko da Tunisiya suka fi ko wacce ƙasa yawan shigar da fina-finai.

Wata sabuwar sashe na wannan taron shi ne, KILAF-SUG Carnival, wadda zai gudana a ranar 8 ga Nuwamba a Filin Wasanni na Adamu Mu’azu, Jami’ar Bayero. Za a gabatar da jerin gwanon al’adu, nunin kaya, durbar da kuma wasannin kiɗa domin nuna ɗaukakar al’adun Afirka.

By ukarofi