Daga AISHA ASAS
Shugaban shiraya taron bajekolin fina-finan harsunan asali na Afirka (KILAF), Alhaji Abdulkarim Mohammed, ya bayyana cewa, ƙungiyarsu na da niyyar ci gaba da ƙarfafa matasa su ci gaba da shirya fina-finai da ke bayyana al’adun Afirka.
Yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishin NUJ na Kano, Alhaji Abdulkarim ya ce an karɓi fina-finai 616 daga ƙasashe 77, kuma an zaɓi 85 daga ciki don baje koli. Ya ce, ƙasashe 14 ne ke cikin waɗanda ke neman lambobin yabo, ciki har da fina-finai da aka haɗa gwiwa da ƙasashen Burtaniya, Amurka, Isra’ila da Italiya.
Ya ƙara da cewa, akwai lambar yabo guda 18 da za a raba ga nasarorin da aka zaɓa daga cikin jerin fina-finai 87 da aka nuna. “Duk da haka, mun yi tsari mai inganci wajen zaɓe wanda ya sa kowane ɗan takara yana da damar ganin kansa a matsayin mai nasara,” inji shi.
Ya bayyana cewa, KILAF ya samar da littattafai shida na bincike da za a yi amfani da su wajen koyarwa a fannin fina-finai da masana’antu. Haka kuma ya sanar da shirin taron ‘Entrepreneurship Summit for Women in Media Business’ karo na biyu, wanda za a gudanar a ranar 8 ga Nuwamba a Makarantar Kasuwanci ta Dangote da ke ƙarƙashin Jami’ar Bayero.
