Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar APC ta ƙara samun sabbin mambobi bayan wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Kaduna guda huɗu da ‘yan majalisar wakilai ta tarayya guda biyar, tare da dubban magoya bayansu, sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar a babban gangamin da aka gudanar a ranar Asabar.
Da wannan sabon sauya sheƙa, APC yanzu tana da ‘yan majalisar wakilai ta tarayya 13 daga jihar Kaduna, yayin da PDP ke da uku kacal. A majalisar dokokin jihar kuma, APC na da mambobi 26, PDP kuma takwas.
An gudanar da gangamin a Filin Murtala Sƙuare da ke Kaduna.
A jawabinsa, Gwamna Uba Sani ya tabbatar wa masu sauya sheƙar cewa APC gida ɗaya ce wadda ba ta nuna bambanci ga mambobinta, yana mai cewa:
“Waɗanda suka shiga jam’iyyarmu yau da waɗanda suka kasance tun asali za su samu irin wannan dama ɗaya. Abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda za ku kusanci talakawa da kuma kula da yankinku da suka zaɓe ku.”
Gwamnan ya tuna cewa APC tana da ‘yan majalisar wakilai huɗu ne a 2023, amma yanzu ta kai 14.
“A yau a Kaduna, ba mu da adawa. Na taɓa gaya wa Shugaba Bola Tinubu watanni da suka wuce cewa muna fatan samun kashi 80 cikin 100 na ƙuri’un Kaduna. Amma yanzu na canja matsayina a 2027, kashi 95 cikin 100 na ƙuri’un Kaduna za su tafi ga APC ne.”
Ya bayyana cewa yawan sauya shekar da ake samu a jihar ba wani abu ba ne illa sakamakon gwamnatinsa wadda ke yin adalci, gaskiya da haɗin kai.
“Jiharmu ita ce mafi ƙabilu a Nijeriya, amma mun yi amfani da wannan bambanci a matsayin ƙarfi. Shi ya sa yau ba mu fuskanci wani rikicin addini ko ƙabilanci ba abin da bai taɓa faruwa ba. Muna aiki a matsayin yan uwa ‘yan gida ɗaya.
Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce APC ta samu cikakken rinjaye a jihar Kaduna, abin da ba wata jam’iyya ba ta taɓa samu ba.
“A yau, ko a Zone 1, Zone 2 ko Zone 3, APC ce jam’iyyar da za a fafata da ita. Ba mu taɓa yin ƙarfi haka ba a baya,” inji shi ga taron jama’a mai yawa.
