
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamishinan Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) na yankin Arewa ta Gabas, Alhaji Abba Jato, ya roƙi Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe da ya fitar da kuɗaɗen lamuran hajji ga hukumar jigilar alhazan jihar domin bata damar biya gabanin wa’adin 21 ga watan Disamba da aka bayar ya ƙare.
Hukumomin Saudiyya sun sanar da ranar 21 ga Disambar 2025 a matsayin lokacin ƙarewar wa’adin da aka ɗiba wa hukumomin alhazai na su biya kuɗaɗen ayyukan hajjin 2026.
Alhaji Abba Jato ya yi kiran ne a jiya Litinin yayin ziyarar ta musamman ga gwamnan, a Gidan Gwamnatin jihar da ke cikin garin Gombe.
Ya ce, biyan kuɗaɗen akan lokaci ga hukumomin na Saudiyya ta hannun NAHCON zai taimaka wajen rage ƙalubale lamuran gudanarwa a yayin ayyukan hajji cikin walwala.
Ya ƙara da cewa, lokacin bada biza ga maniyyata zai ƙare ne a ranar 2 ga watan Fabarairu, 2026, yana mai kira ga jihar da ta bada haɗin kai domin kauce wa shiga matsala.
Dacyake jawabi a madadin gwamnan, Sakataren Gwamnatin jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ya jaddada aniyar gwamnatin ta cigaba da taimaka wa harkokin hukumar don ganin ta cika sharuɗɗan da ake buƙata akan lokaci.
