Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta tabbatar da sababbin jagororin tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya aika da wasiƙa ga Majalisar Dattawa, inda ya nemi da ta tabbatar da naɗin sababbin shugabannin rundunonin tsaro da ya yi a kwanan nan.

Takardar ta ƙunshi sunayen manyan hafsoshin da aka zaɓa domin jagorantar rundunonin soji, ƴan sanda da sauran ɓangarorin hukumomin tsaro na ƙasa.

A ƴan kwanakin nan ne Tinubu ya yi wa ofisoshin jagororin tsaron garambawul ciki har da tsige Janar Christopher Musa Gwabin a babban hafsan tsaro da maye gurbinsa da Janar Olufemi Oluyede, wanda shi ne shugaban sojojin ƙasa gabanin haka.

A cewar mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, sauyin wani ɓangare ne na inganta fannin tsaro da gwamnatin tarayya take yi da nufin daƙile ƙalubalen da fannin ke fuskanta.

By Babaji