Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kwamandan Hisbah na Jihar Katsina, Sheikh Dr. Aminu Usman (Abu Ammar) ya bayyana haka a wajen taron ƙarawa juna sani da aka shirya wa malamai kan addinin Musulunci a Katsina.
Dr Ammar ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu ‘yan kasuwa ke aikata rashin gaskiya wajen tauye mudu da sauran awo.
Ya danganta wasu daga cikin matsalolin tattalin arzikin da sauran bala’o’i da ake fuskanta a yau da irin wannan ɗabi’ar ta yin almundahana da ma’auni da awo a tsakanin ‘yan kasuwa.
Sheikh Abu Ammar ya ƙara da cewa, la’akari da yadda matsalar ta yaɗu a cikin al’umma, Gwamnatin Jihar Katsina ta bayar da umarnin amfani da awo da ma’aunin da hukumar ta amince da su domin daƙile wannan matsala.
Ya tunatar da jama’a cewa hukumar ce ke da alhakin tabbatar da bin ƙa’idojin addinin Musulunci, inda ya gargaɗi duk ɗan kasuwan da ya ƙi amfani da awo na hukuma cewa zai fuskanci hukunci.
Haka kuma ya yi kira ga malamai da su ba da goyon baya wajen wayar da kai don cimma manufofin da aka sa gaba
A nasa bangaren, sakataren dindindin na ma’aikatar, Alhaji Abdulaziz Abdu Umar, ya bayyana shirye-shiryen ma’aikatar na yin aiki tare da hukumar Hisbah domin daƙile matsalar.
A ƙasidun da aka gabatar daban-daban, Shaikh Naziru Kofar Baru Daura da Shaikh Goni Nasiru Adam Funtua sun gabatar da kasidu masu taken “Koyarwar Musulunci Kan Ma’auni da Awo: Amfani A Cikin Kasuwanci da Halayyar Al’umma” da “Gaskiya a Kasuwanci, Tsabtace Al’umma: kula da ƙa’idojin Musulunci Kan ma’auni da awo.”
Taron ya samu halartar wakilan ƙungiyoyin kasuwanci, JIBWIS Da’awa, Family Support Al-Ihsan Jindu, Da’awa Darika, Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Mata, da sauran masu ruwa da tsaki a fadin jihar da jami’an tsaro da ƴan jarida.
