‘Yan APC da dama sun sauya sheka zuwa NNPP a Bichi

Spread the love

Wasu ‘yan jamiyyar APC mazaɓar ‘Yallami dake garin Beguwa a ƙaramar hukumar Bichi, sun miƙa wuya ga shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, inda suka sauya sheka daga jam’iyyarsu zuwa jam’iyyar NNPP.

A wata sanarwa da jama’ar yaɗa labarai ta ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa manema labarai, ‘yan jamiyyar APC sun bayyana sauya shekar ne, a yayin da suka kai ziyara ga shugaban ƙaramar hukumar a ofishinsa dake sakatariyar Bichi.

Jagoran miƙa su ga shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, Sama’ila Idris, ya bayyana cewa, sakamakon gina sabuwar makarantar firamare da majalisar ƙaramar hukumar ta yi ne a yankinsu, wadda shekaru masu yawa a baya suka sha fafutarkar neman a yi musu, ba a yi ba, sai yanzu a wannan gwamnatin mai ci, shi ya sa suka dawo jam’iyyar NNPP kacokan.

Shi kuwa shugaban masu sauya shekar, Rabi’u Idris Beguwa ‘Yar Bodo, ya ce, tawagar tasu ba su ke nan ba, nan gaba kaɗan za su yi gangami na waɗanda suka yi mubayi’a, zuwa ga fadar shugaban majalisar ƙaramar hukumar tare da bijiro da wasu buƙatun nasu ga gwamnati.

Shugaban ƙaramar hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya yi farin ciki da jin daɗi, inda ya karɓe su hannu bibiyu, sannan ya ja hankalinsu, su tabbatar sun sa ‘ya’yansu a wannan makaranta da ya yi, kuma su kula da karatunsu ta hanyar zuwa makaranta koda yaushe a kan kari, domin ilimi shi ne ƙashin bayan rayuwar ‘yan’adam baki ɗaya.

Daga bisani kuma ya yi musu alƙawarin gina musu asibiti a santar dake tsakanin unguwannin Dunawa, Beguwa, ‘Yar Bodo domin sauƙaƙa wa al’umar yankin yayin da suka buƙaci zuwa asibiti ta fuskar taimakon gaggawa domin inganta lafiyarsu.

By ukarofi