Gwamnatin Tarayya ta nanata ƙudirin farfaɗo da sashen ma’adanai domin rage dogaro da man fetur

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamnatin Tarayya ta sake tabbatar da aniyarta ta bunkasa sashen ma’adanan kasa a matsayin wani ɓangare na yunƙurin rage dogaro da kuɗaɗen man fetur, da kuma ƙara ƙarfin tattalin arzikin ƙasa tare da samar da ayyukan yi ga ’yan ƙasa.

Wannan jawabi ya fito ne a yayin taron wayar da kai kan aiwatar da sabon tsarin bayanan ma’adanan ƙasa na yankin Arewa maso Yamma, wanda ya gudana a Kano, ranar Litinin.

A jawabinsa, Kwamishinan Tarayya mai wakiltar Jihar Kano a Hukumar Raba Kuɗin Shiga ta ƙasa (RMAFC), Alhaji Adamu Fanda, ya bayyana cewa Allah Ya yi wa Nijeriya yalwar ma’adanai daban-daban da ke buƙatar kula ta musamman da tsari ingantacce domin su taka rawar gani wajen bunƙasa tattalin arzikin kasa.

Ya ce Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakan inganta tsafta, gaskiya da doka a aiwatar da hakar ma’adanai, tare da tabbatar da bin ƙa’idojin rarraba kuɗaɗen shiga cikin tsarin gwamnati.

Ya ƙara da cewa, “Lokaci ya yi da Nijeriya za ta mayar da hankali wajen haɓaka sashen ma’adanai don bunkasa tattalin arziki da samar da guraben ayyukan yi ga matasanmu.”

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda Kwamishinan Ma’adanai na Jihar Kano, Alhaji Hamza Safiyanu Kachako ya wakilta, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da hadin gwiwa da Gwamnatin Tarayya domin aiwatar da sauye-sauye masu amfani a sashen ma’adanai.

Gwamnan ya ce Jihar Kano na ɗaukar matakai na gano da kuma tantance wuraren hakar ma’adanai domin tabbatar da bin dokoki da ƙa’idoji na kiyaye muhalli da tsarin hakar ma’adanai mai ɗorewa.

Shi ma a jawabin nasa, Shugaban Hukumar RMAFC, M.B. Shehu, wanda Ozo Obunneme Obodougu ya wakilta, ya bukaci masu ruwa da tsaki da hukumomin gwamnati su haɗa hannu wuri ɗaya don ganin duk wani kudin shiga da ya kamata ya shiga Asusun Tarayya daga ɓangaren haƙar ma’adanai ya kasance ya isa ba tare da ɓata ba.

Ya jaddada cewa haɗin kai, gaskiya wajen bayar da bayanai, da kuma sa ido mai inganci sune manyan dabarun tabbatar da cika burin tattalin arzikin ƙasa.

By ukarofi