
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta mayar wa Shugaba Donald Trump na Amurka martani kan kalamansa na zargin kisan kiyashi ga al’ummar Kiristoci a Nijeriya, yana mai cewa ƙasar tana aiki tuƙuru wajen bada kariya ga ƴancin yin ibada ga dukkanin ƴaƴanta da ke sassan ƙasar.
A jiya Juma’a ne Trump ya wallafa wani rubutu ta kafar Soshiyal Mediya, inda ya ayyana Nijeriya a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da ake da damuwa akansu, sannan ya kuma zargi cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla.
Saidai, da yake tsokaci akan al’amarin ta kafar sada zumunta, Tinubu ya yi watsi da zargin Shugaban Amurkan, yana mai bayyana su a matsayin abinda ba gaskiya ba ne, a cewarsa hakan cutarwa ne ga darajar Nijeriya a idon duniya.
Ya bayyana cewa, tunda ya kama aiki a 2023, gwamnatinsa tana ƙoƙarin haɗa kan jagororin addinin Musulunci da na Kiristanci domin tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu da kuma ƙoƙarin warware ƙalubalen tsaro da ke addabar al’umma ba tare da la’akari da addini ba.
Ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta cigaba da martaba addinai, wanda dokar ƙasa ta bada ƴancin gudanarwa acikin al’umma sannan tsare-tsarensa suna tafiya da su kafaɗa-da-kafaɗa.
Shugaba Tinubu ya kuma tabbatar wa ƙawayen Nijeriya a mataki na ƙasa-da-ƙasa ciki har da Amurka cewa ƙasar a shirye take ta ƙarfafa haɗin kai mai ƙarfi domin bai wa garuruwa marasa galihu kariya daga tashin-tashina da hare-haren ƴan ta’adda.
