Zargin kisan Kiristoci: Mu na girmama ‘yancin addinai, inji Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan jawabin Shugaban Amurka Donald Trump kan zargin kashe kiristoci a Nijeriya.

Trump ya ayyana Nijeriya a cikin jerin ƙasashen da ake da damuwa akansu kan wasu al’amura masu cutar ga al’umma.

Ya ce, kiristanci na fuskantar babbar barazana a Nijeriya, inda ya ƙara da cewa ana kashe dubban Kiristoci, kuma masu tsaurin kishin Islama ne ke aikata wannan kisan gillar.

Bugu da ƙari, Trump ya ce ya bai wa ƴan majalisar wakilai Riley Moore da Tom Cole umarnin fara bincike kan hakan kuma su kai masa rahoton sakamakonsa da zarar sun kammala.

A wata sanarwa da Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, ya ce, “duk da cewa Najeriya na godiya da kulawar da ƙasashen duniya ke ba ta musamman kan batun haƙƙin ɗan’adam da haƙƙin addini, wannan batun na zargin kashe kiristoci a ƙasar ba haka ba ne.

Duk ƴan Najeriya suna suna da ƴancin gudanar da addininsu yadda ya kamata, kuma suna gudanar da ibadarsu ba tare da tsangwama ba.”

Sanarwar ta ce a ƙarƙashin mulkin Tinubu, gwamnatinsa na ƙoƙari sosai wajen yaƙi da ta’addanci da ƙarfafa gwiwa da kare rayuwar al’umma ba tare da nuna bambanci.

Gwamnatin ta ce, Nijeriya za ta cigaba da tattaunawa da Amurka da ƙasashen duniya domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a sassanta.

By Babaji