PDP ta dakatar da sakatare, mai bada shawara kan harkar shari’a da wasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar jam’iyyar adawa, PDP, ta dakatar da Sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, wanda na hannun dama ne ga Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Haka kuma, ta dakatar da wasu shugabanninta da ake ganin suna da alaƙa da tsohon gwamnan na Jihar Ribas.

Sakataren yaɗa labaranta, Debo Ologunagba ya ce jam’iyyar ta ɗauki matakin ne wanda za a yi tsawon wata guda aciki, jim-kaɗan bayan gudanar da taron gaggawa na kwamatin gudanarwa a yau Asabar.

Sauran waɗanda aka dakatar sun haɗa da mai ba jam’iyyar shawarar kan harkar shari’a, wato Kamaldeen Ajibade (SAN) da sakataren tsare-tsare Umar Bature da kuma mataimakin babban lauya.

Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da PDP daga gudanar da babban taronta na ƙasa da ta shirya gudanarwa a birnin Ibadan na jihar Oyo a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba.

Daga bisani jam’iyyar ta ce za ta cigaba da shirye-shiryen gudanar da taron a daidai lokacin da ta ɗaukaka ƙara ƙasa da kwana da hukuncin kotun.

By Babaji