Ƙungiyar Arewa Think Tank ta caccaki Trump kan ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa akanta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta yi alla-wadai da Shugaba Donald Trump na Amurka kan kalamansa na ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa akanta wato ‘CPC’, tana mai bayyana hakan a matsayin yunƙurin amfani da lamarin addini wajen haddasa fitina a ƙasar.

A wata sanarwa da ta fitar a Kaduna ta hannun muƙaddashinta, Muhammad Alhaji Yakubu, ATT ta zargi duniyar Turawan Yamma da amfani da addini don cimma manufarsu ta raba kan ƴan Nijeriya bayan sun yi amfani da wasu hanyoyi a baya ba su yi nasara ba.

“Mun yi tir da matsayar duniyar Turawan Yamma ta haddasa rikicin addini a Nijeriya, wajen amfani da wasu mutanenmu a matsayin abokan hulɗa”, inji Yakubu.

ATT ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da kada ta ruɗu da tare da faɗawa cikin tarkon,, tana mai gargaɗin ire-iren mutanen da su ƙaurace wa haɗa baki da ƴan waje wajen cutar da al’ummarsu da ma ƙasa baki ɗaya.

Kazalika, ya ce ikirarin Donald Trump cewa ana yi wa Kristen kisan kiyashi a Nijeriya ba haka ba ne, a cewarsa, tsawon shekaru al’ummar musulmi da kirista suna zama cikin zaman lafiya da fahimta, da girmama juna a tsakaninsu.

By Babaji