Ƙungiyar Malaman jami’ar UMYU a Katsina ta tsunduma yajin aiki

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ƙungiyoyin malamai da ma’aikatan Jami’ar Ummaru Musa Yar’adua (UMYU) a Katsina sun tsunduma yajin aiki “sai badba ta gani” daga yau Litinin, 3 ga watan Nuwamba.

Yajin aikin ya shafi dukkan malamai da ma’aikatan jami’ar, sakamakon wasu matsalolin da suke zargin gwamnati ta yi biris da su.

Daga cikin ƙorafe-ƙorafen da suka gabatar sun haɗa da; Rashin ingantaccen jin daɗin ma’aikatan jami’ar, Matsalar ƙwace ikon gudanar da shafin (portal) na makaranta.

Sauran sun haɗa da ƙarancin kuɗaɗen gudanarwa, da kuma batun walwalar ɗalibai.

Sai dai a nata ɓangaren, Gwamnatin Jihar Katsina ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafen ƙungiyar, tare da jaddada cewa tana ci gaba da ƙoƙarin magance dukkan matsalolin da suka shafi jami’ar da cigaban ilimi a jihar.

By ukarofi