Gwamna Uba Sani ya ƙaddamar da gidaje 100 ga waɗanda hare-haren ‘yan bindiga ta shafa

Spread the love

Gwamnatin Jihar Kaduna da haɗin gwiwar rukunin kamfanin Ummi International Nigeria Ltd (UINL) da kamfanin Family Homes Funds (FHFL), bisa tallafin ma’aikatar kasafi da tsare tsare ta Najeriya sun gina gidaje 100 ga mutanen da rikici ya raba da muhallansu da sauran marasa ƙarfi.

Gidauniyar Ummi International Nigeria Ltd ce ta samar da katafaren filin, a inda gwamnatin Kaduna da Family Homes Funds har ma da haɗin gwiwar ma’aikatar kasafi da tsare tsare ta tarayyar Najeriya suka ɗauki nauyin ginin.

Da yake jawabi a yayin ƙaddamar da miƙa gidajen waɗanda ke yankin Rigachikun, Gwamna, Sanata Uba Sani, ya ce sun yi wannan aiki ne domin rage musu raɗaɗin iftila’in da ya same su.

A nasa ɓangaren ministan ma’aikatar kasafi da tsare tsare, Alhaji Atiku Bagudu, ya bayyana cewa ma’aikatar za ta ci-gaba da aiki da kamfanoni masu zaman kansu da sauran ƙungiyoyin sa kai domin kaiwa ga cikakkiyar Nasara.

Itama tsohuwar ministar mata ta Najeriya, Mista Pauline Talen, ta yaba wa dukkan ɓangarorin da suka haɗa gwiwa wajen samar da gidajen, waɗanda za su taka muhimmiyar rawa a rayuwar waɗanda suka amfana.

Dakta Umma Sani (Zinariyar Gabasawar Zazzau), ita ce Shugabar Gidauniyar Ummi International Nigeria Ltd, ta ce sun jima suna wannan aiki na samarwa zawarawa da marayu matsuguni domin inganta rayuwar su kamar ta masu iyaye.

Haka kuma ta yaba wa Gwamnan Kaduna, a bisa yadda ya bawa shirin cikakkiyar gudunmawa da ta kai ga samun wannan nasara.

Ambasada Dakta Fatima Mohammed Goni, ita ce Shugabar GBNI, ta ce babu shakka Hajiya Umma ta zama madubi a tsakanin matan Najeriya, la’akari da yadda ta assasa wannan aiki na jin ƙai ga rukunin al’umma masu tsananin buƙata.

A ƙarshe Goni ta yi fatan waɗanda suka amfana da gidajen za su alkinta su, ta yadda zai zama an cimma manufar samar da shi.

Taron ya gudana ne a yau Litinin, inda ya sami halartar masu ruwa da tsaki daban-daban na Jihar Kaduna.

By ukarofi