Abdulsalami Abubakar ya kirayi ƴan Nijeriya su dunƙule wajen kare martabar ƙasa ga barazanar ƴan waje

Spread the love

Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritayal), wato tsohon Shugaban ƙasa na mulkin soja a Nijeriya, ya buƙaci shugaban Amurka Donald Trump da ya goyi bayan yaƙin da Nijeriya ke yi da ta’addanci da rashin tsaro ba wai yi mata barazana ba.

Abdulsalami, wanda a yanzu yake Landon, ya yi magana a wata hira ta wayar tarho, inda ya ce ya lura cewa kalaman shugaban na Amurka ka iya kawo cikas ga haɗin kan ƴan Nijeriya.

Ya kuma bukaci ƴan Nijeriya da su yi watsi da bambance-bambancen da ke tsakanin su, su haɗa kai don kare ƴancin ƙasar ta hanyar fuskantar barazana daga ƴan ƙasashen waje a tare.

Ya kara da cewa “dole ne haɗin kai, hikima, da difulomasiyya su kasance gaba da rarrabuwar kawuna a wannan mawuyacin lokaci.”

Kazalika, ya ce akwai buƙatar tattaunawa da Trump domin tinkarar wannan batun da kuma kawar da irin wannan barazanar don nan gaba.

By Babaji