
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Dokoki ta ɗauki mataki mai ƙarfi wajen inganta yaƙi da cin zarafin ɗalibai mata a manyan makarantu, yayin da ƴaƴanta suka amince da yin shekaru biyar mafi ƙaranci da 14 mafi yawa a kurkuku ga lakcarori da ma’aikatan da aka samu da hannu a lamarin.
A ranar Laraba Majalisar Dattawa ta tabbatar da ƙudirin dokar wanda ya shallake karatu na ƙarshe a wajenta bayan kamala aiki akansa daga Majalisar Wakilai.
Daga nan sai suka yi aiken sa ga Shugaba Bola Tinubu domin amincewa da sanyawa a kundin doka don fara aiki a nan take.
Ƙudirin ya ƙunshi sashe masu yawa na cin zarafi da ka iya sa a hukunta wanda aka samu da hannu a ciki waɗanda suka haɗa da: neman aikata alfasha da nufin taimaka musu a jarrabawa, tsoratarwa, barazana, samar da yanayin karatu mai tsauri, taɓe-taɓe, riƙe hannu, runguma, sumbata, aiken bidiyoyin batsa ko hotuna ko saƙonni ko barƙwancin da suka shafi haka ko kuma tsokaci akan surar jiki ko tozartawa akai-akai.
Haka kuma, ƴan majalisar sun tirje akan ba za a bada zaɓin biyan tara ba ga wanda aka kama da laifin a madadin zuwa kurkuku a yunƙurinsu na hana aikata munana da miyagun ɗabi’u domin kare ɗalibai marasa galihu da ke karatu a sassan ƙasar.
Sannan, wani sashe na ƙudirin, ya bai wa ɗalibai ko wakilansu damar neman a yi musu adalci a yayin da malamai suka zalunce su ko da bayan an yi musu hukunci.
Domin tabbatar da tsare gaskiya da adalci, ƙudirin ya wajabta wa dukkanin manyan makarantu samar da kwamitin dokar hana cin zarafi da zai riƙa kula da ƙorafe-ƙorafe akan abinda ya shafi lamarin.
Kazalika, ƙudirin ya haramta wa makarantu ɗaukar mataki na cikin gida akan irin batun matuƙar aka gabatar wa kotu domin kauce wa rufa-rufa.
Har’ilayau, ƙudirin ya hukunta a riƙa kai ƙorafi ga hukumar ƴan sanda, Antoni Janar da kuma kwamitin kula da lamarin na makarantar da abin ya shafa.
