FCCPC ta rufe shagunan tufafi a Kano saboda yaudarar masu saye

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar kare haƙƙin mai saye ta ƙasa wato Federal Competition and Consumer Protection Commission
(FCCPC) ta gudanar da samame ranar Laraba a Kano, inda ta rufe wasu shagunan dillalan kayan ɗinki da ake zargin suna sayar da kayan da aka tauye mudun su.

Binciken da hukumar ta yi ya gano cewa wasu ƴan kasuwa na sayar da kayan da aka rubuta “10 yards” yadi goma alhali ba su wuce idan ka duba ciki sai ka samu bai wuce yadi tara ba, “9 yards”, tare da karɓar cikakken kuɗi daga masu saye.

Daraktar bincike da Sa-ido ta FCCPC, Boladale Adeyinka, ta bayyana cewa wannan aiki na karya dokar FCCPA ta 2018, musamman sashe na 123 da 125, wanda ke hana sayar da kaya da bayanan ƙarya.

Hukumar ta ce irin wannan yaudara tana cutar da masu saye, tana kuma jefa sahihan ‘yan kasuwa cikin matsin tattalin arziki.

Adeyinka ta ce duk wanda aka kama da laifi, ana ɗaure shi daga shekara 5 zuwa 10, ko tara daga Miliyan 5 zuwa miliyan 100 ko a haɗa wa mutum gaba ɗaya.

Shi ma lauyan hukumar na yankin Arewa maso Yamma, Malam Jamilu Mohammed, ya ce wannan mataki zai taimaka wajen kawar da kaya marasa inganci daga kasuwanni.

Hukumar ta yi gargaɗin cewa za ta ci gaba da ɗaukar mataki kan duk mai aikata irin wannan laifi, tare da kira ga jama’a su riƙa kai rahoton duk wani abu da ke nuna ƙarya ko ruɗi a kasuwa.

Shagunan da aka rufe sun haɗa da waɗanda ke kan titin Ajasa, Inuwa Wada Road, Ibrahim Taiwo, Gandun Albasa da kuma Sharaɗa a Kano.

By ukarofi