Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Bayan shekaru kusan saba’in na jiran a gyara hanya, al’ummar Tamburawar Gabas a karamar hukumar Warawa sun samu gagarumar farin ciki bayan Shugaban ƙaramar Hukumar Warawa, Hon. Lamido Sunusi Ahmad, ya kammala gina musu hanya da ta dade tana janyo musu matsala.
Jagoran al’ummar garin, Alhaji Bala Tamburawa, ya bayyana cewa wannan hanya ta kasance mafarkin jama’a shekaru da dama, inda aka sha nema a lokutan da suka gabata amma babu wanda ya aiwatar. Ya ce, “Mun shafe shekaru da dama muna neman wannan hanya, sai yanzu Allah ya kawo mana wannan hazikin shugaba da ya ceto mu daga wahala.”
A cewar Bala Tamburawa, hanyar tana da muhimmanci saboda tana hada mazabu hudu – daga Kuma Galadima, ta wuce Tamburawar Gabas, zuwa Yanagar, inda ta hade da Madari. Ya ce hakan zai bunƙasa tattalin arzikin yankin da sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da kayayyaki.
Da yake mayar da martani, Hon. Lamido Sunusi Ahmad ya gode wa jama’ar Tamburawa bisa ziyartar sa da nuna godiya, yana mai cewa wannan aiki ne da ya daɗe yana cikin jerin ayyukan raya ƙasa na karamar hukumar. Ya ce, “Wannan hanya ita ce farkon cigaba, nan gaba za mu gina asibitin shan magani da samar da wutar lantarki domin bunkasa yankin.”
Ya kuma jinjinawa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa yadda yake baiwa shugabannin ƙananan hukumomi cikakken goyon baya wajen gudanar da ayyukan ci gaban jama’a.
Hon. Lamido ya tabbatar da cewa gwamnatin ƙaramar hukumar Warawa za ta ci gaba da yin ayyukan da za su kawo sauyi mai ma’ana ga rayuwar al’ummar yankin.
