“Rubutu makami ne mai dafi da za a iya sokar ahalin marubuci da shi”
Daga AISHA ASAS
Shafin Adabi na wannan mako ya saƙulo wa masu karatunmu ɗaya daga cikin jajirtattun matasan da ke yi wa adabi hidima. ƙoƙarin sa da nacewa wurin ganin ya kwankwaɗe duk wani ƙalubale da ya yi tuntuɓe da shi a hanyar sa ta zama marubuci abin a yaba masa ne.
Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Faisal Haruna Hunkuyi;
MANHAJA: Za mu so ka fara da bayyana kanka ga masu karatunmu.
FAISAL HUNKUYI: Sunana Faisal Haruna Hunkuyi. An haife ni a cikin garin Hunkuyi da ke ƙaramar Hukumar Kudan a Jihar Kaduna. Na yi primary da secondary school ɗi na duk a garin Hunkuyi kafin in wuce Jami’ar Jihar Kaduna (Kaduna State Uniɓersity) inda anan na samu shaidar kammala digiri na farko a ɓangaren noma da kiwo tare da tsare-tsaren shige da ficen kayan noma (General Agriculture). Ta ɓangaren Islamiyya nan ma an sha fafutuka ƙwarai har kawo yanzu kuma akan doron fafutukar ake.
Kasancewar rubutu na da rassa da yawa. Za mu so sanin ɓangaren da ka fi ƙwarewa.
Mafiyawancin rubutuna na fi maida hankalina akan yadda zamantakewa a gidajen ma’aurata ke yin tsami; na kan shiga in zaƙulo wani abu da ya kan zama silar ruruwar wutar da ke yaɗuwa a cikin gidaje domin in nusar da ɓangaren da abin ya shafa. Duk da yawancin masu karanta rubutuna suna yi min tambayar ‘ni likita ne?’ Ba komai ya sa suke yi min wannan tambayar ba kuwa illah ganin duk takardar da zan ɗora alƙamina a kanta to na kan yi ƙoƙarin shigo da wata cuta da ta addabi al’umma in warwareta sannan in kawo mafita.
Ka yi zancen makaranta littafanka na yawan tambayar ko kai likita ne. Shin ta yaya ka ke iya samar da gamsashen bayyanai kan harkar lafiya alhali kai ɗin ba likita ba ne?
Ina samar da gamsasshen bayani ta hanyar tuntuɓar ƙwararrun likitoci kasancewar ina da kyakkyawar fahimta tsakanina da su, idan na ɗauki wani ɓangaren har asibiti ina zuwa in gani da idunana sannan in yi tambaya.
Ko za ka kai mu ga lokacin da ka fara ɗora alƙalami da zumar rubuta labari?
Na fara ɗora alƙalami a bisa takarda tun 2008, ina JSS 2 a lokacin. Sai dai rashin ƙarfin gwiwa da ban samu ba tare da yadda abokaina suke yi min dariya ya sa na watsar da harkar. Duk da a lokacin idan na rubuta kuma su kan zo su ɗauka su karanta har tambayoyi su biyo baya. Ba zan manta ba akwai mahaifiyar wani abokina idan ta ji suna yi min dariya ta kan kira ni har ta karɓi aikin da na yi ta karanta sannan ta fara jinjina min, ba ƙaramin daɗi na ke ji ba a lokacin.
Waɗane ƙalubale ka fuskanta kafin burin naka na zama marubuci ya tabbata?
ƙalubale fa kam an haɗu da su birjik, sai dai wani ya fi wani kawai.
Na farko; Na fara rubutu ban san kowa ba haka babu wanda ya sanni duk da lokacin da na fara Facebook 2012 na yi matuƙar ƙoƙari wajen bibiyar marubutan da ludayinsu ke kan dawo a wancan lokacin. Sai dai kwalliya bata biya kuɗin sabulu ba. Yawancin marubutan da na bibiya da zarar na je da ƙoƙon bara ta basa sake yi min magana wannan ya sa harkar ta ƙara fita a raina. Akwai wanda a satin da ya wuce ma na buɗe ‘messenger’ ina bincike na ci karo da saƙon da na fara tura masa wallahi har yanzu bai buɗe ba balle ya bani amsa.
Na biyu; A lokacin da na ke ganin burina na zama marubuci ya kusa cika, a lokacin kuma ba ni da zaɓin da ya wuce in yi haƙuri kasancewar na koma jami’a sannan ina ganin haɗa taura biyu a bakina ba zai ba ni sakamako mai kyau ba.
Na uku; A yanzu ƙalubalen bai wuce yanayin yadda ake shigar da labaran ba bayan an rubutasu tun daga ‘Online’ ɗin har ‘Publishing’ ɗin kowanne cike yake da na shi salon ƙalubalen.
Idan na fahimce ka babu marubucin da ya taɓa ba ka taimako a lokacin da ka ke fafutukar zama marubuci?
A wancan lokacin gaskiya babu, sai a shekarun da ba su uku zuwa huɗu ba da Allah ya Tarawa garina nono na yi gam-da-katar da wasu zaƙaƙuran .arubuta guda biyu a lokuta mabambanta. Kowanne a cikinsu na bayyana masa burina kuma suka amsheni hannu bibbiyu tare da ƙarfafa min gwiwa don ɗaya a ciki gar da alƙawarin zai shige min gaba wajen wallafa labarina na farko. Dayan kuwa ya yi matuƙar ƙoƙari wajen ajiye duk wasu ayyukansa ya bibiyi rubutuna inda ake buƙatar gyara ya gyara inda kuma ake buƙatar shawara ya bani. Kuma har kawo yanzu ko tari zan yi indai a harkara adabi waɗannan mutum biyun sai sun tuntuɓi dalili.
Shin kana buga labaranka zuwa littafi ko kuwa a iya onlayin ka tsaya?
Ina buga su a takarda sannan ina dillancinsu onlayn.
Zuwa yanzu ka rubuta littafai nawa?
Dogayen labarai za su kai guda biyar sai dai guda ɗaya ne na buga shi a takarda sannan yanzu haka ina shirin fitar da wani a wannan lokacin In sha Allah.
Akwai; ‘Makauniyar Zuciya’, ‘Kisan Boko’, ‘Bahaguwar Rayuwa’, ‘Bokiti Mai Yoyo’, ‘Duniyar Gizo’, ‘Son Zuciya’.
Ko za ka sanar da mu abinda biyu daga cikinsu ya ƙunsa?
Akwai ‘Makauniyar Zuciya’ wanda labarin wasu masoya ne da su ka jima suna dakon soyayyar junansu sai da aka zo gaf da cikar burinsu gwajin jini (Genotype) ya kawo masu cikas. Tun daga asibitin suka lalata sakamakon da aka ba su, abokinsa da ya yi masu rakiya suka bata sakamakon tunatar da shi illar da ke tattare da abinda su ke shirin yi. Sun ɓoyewa kowa har aka ɗaura musu aure. Rayuwar aurensu gwanin ban sha’awa har zuwa lokacin haihuwa ta fara yi musu sallama kuma suka fara da abinda ake hango musu a jere sun haifi yara biyu masu ɗauke da amosanin jini. ɗaya ya mutu ya bar ɗaya, tsananin talauci da wahalar da suke ciki ya sa mijin ya gudu ya bar matar da yarinyar a gadon asibiti, hakan ya harzuƙa iyayenta har suka raba ta da tilon yarinyar da ke kwance tsakanin mutuwa da rayuwa. A ƙarshe dai sun dawo sun haɗu bayan wasu shekaru.
‘Kisan Boko’; Labarin wata ce da ba ta nemi komai ta rasa a duniya ba sai abu ɗaya da ya yi mata bayan ta same shi kuma ta banzatar da shi shi ne; Aure. Ta daɗe tana yi wa kanta huɗuba da “Ba a haɗa gudu da susan katara” ta biyewa kyawun jiki da cincirindon samarin da ke faman fareti a ƙofar gidansu ko yaushe. Ta ba karatun boko muhimmanci fiye da komai har zuwa lokacin da ta gama digirin farko ta fara na biyu. Ta fara kuka da idanuwanta a lokacin da ta nemi samarin nan ta rasa ga tsufa ya doka sallama.
Ko rashin samun goyon bayan manyan marubuta ga marubuta masu tasowa zai iya kawo tawaya a cigaban harkar rubutu?
Gaskiya sosai yana kawowa ne ma ba wai zai kawo ba. Domin ko ranar Alhamis na yi magana da wata da ke da burin fara rubutu sai dai abinda ke sagar mata da gwiwa ta bibiyi manyan maruta da dama amma babu wanda ya saurareta. Sannan, akwai wani ‘conference call’ da aka haɗa a wani guruf a manhajar whatsapp an samu aƙalla mutane biyar da suka shigar da ƙorafi makamancin wannan.
Kin ga kenan rashin samun goyon bayan manyan da suka jima a fagen ba ƙaramin tawaya zai kawo a fuskar rubutu ba.
Wa ake cewa marubuci?
Marubuci wani mutum ne wanda yake nazari da binciken rayuwa da halayyar jama’ar da yake zaune tare da su, sannan kuma ya ɗabbaƙa rubutunsa domin fayyace ainihin daidaitacciyar hanya wacce kowa ya kamata ya bi. Marubuci yana da wata baiwa ta musamman da Allah ya ba shi, wacce da ita ne yake iya tsara maganganun da za su nusar da makarancin rubutunsa illar wani abu da ya yi masa karan tsaye a zuciya. Marubuci yakan yi tunani irin na mutane da dama, walau bai taɓa rayuwa a cikin su ba, ko kuma akasin haka.
Marubuci wani madubi ne mai ɗauke da majigin nazarto wani abu da zai faru ko kuma ya taɓa faruwa a wani ƙarni na can baya sannan ya kan iya hasashen abinda zai faru a gaba ma.
Idan da za a ba ka damar kawo sauyi a matsaloli da ke ci wa marubuta tuwo a ƙwarya, wacce matsala ce ka ke ganin za ka kawo hanyar magance ta?
Akwai matsalolin da ke ci wa marubuta tuwo a kwarya birjik amma matsalar da na ke hangenta a babbar matsala duk da wasu za su kalle ta a ba ta kai ta kawo ba ba ta wuce; ‘Yan ‘downloading’ ba, idan na ce ‘yan ‘downloading’ ina nufin ma su zuwa su ɗauki littafi ba tare da izinin marubuci ko marubuciyar ba su karanta shi da muryoyinsu domin gyara tukunyar gidansu kinga anan an yi kura da shan bugu gardi da kwasar kuɗi. Idan ki ka je YouTube za ki samu littattafan marubuta sosai waɗanda ba su da masaniyar yadda aka fara karantasu har aka ɗora a YouTube ɗin ma. Wannan ba ƙaramin koma baya ba ne ga marubuta duk da salo ne na ci gaban zamani. Kuma samun ‘audio’ ɗin da ake yi ya taka muhimmiyar rawa wajen daƙile karatu a takarda ko a onlayin ɗin ma.
A mahangata hukumomin da abin ya shafa yakamata su yi tsayin daka wajen daƙile yawaitar wannan matsalar kamar yadda ‘yan fim su ka dinga fafutuka a lokacin da su ka fuskanci makamancin wannan matsala ta satar fasaha.
Na biyu; Yadda kasuwar littafi ke tafiya a onlayin ɗin shi ma akwai gyara sosai domin ni har na gwammace ma in samu masu siyen labarina a takarda in buga in ba su su bani sulallana akan in kai shi onlayin. Dalilina kuwa shi ne; marubuci ko marubuciya za su ɓata dare wajen tsara rubutunsu a ƙarshe a onlayin ɗin idan ba za su bada na bulus ba bai wuce mutum uku zuwa biyar ne za su iya cire kuɗi su siya, waɗannan mutane biyar ɗin idan su ka siya to ki ƙaddara tamkar kin sakarwa duniya labarin ne. Akwai marubuciyar da ke bani labarin har ‘group’ ake buɗewa da ake tura irin waɗannan labaran da ake siyarwa.
A wannan gaɓar in da zan samu dama zan ƙirƙiri wata manhaja ce da za a riƙa saka littafi a ciki tana ba da lambobin sirri mabambanta (password) ta yadda idan Bala ya siya to lambobin da zai sa ya buɗe littafin ya bambanta da na Shehu. Sannan a cikin manhajar zan saka abin da zai hana littafin buɗewa a ko wacce waya face ainihin wayar da aka fara buɗe shi da ita. Faruwar hakan zai daƙile yawaitar tura labarin da aka siya ba tare da izini marubuciyar ko marubucin ba.
A wane yanayi ka fi jin daɗin yin rubutu?
Ina jin daɗin rubutu a lokacin da na ke halin kaɗaici, babu dare ko rana ko yaushe matuƙar zan kasance ni kaɗai a wurin da babu hayaniya kuma bani da wani aiki, to tabbas; zan ɗora alƙalamina akan takarda.
Ta ya ka ke samun jigon rubutu idan za ka yu?
Akwai hanyoyin samun jigo da yawa, domin idan ki ka kalli rayuwarmu ta yau da kullum zagaye mu ke da mabambantan jigon da suke buƙatar a taɓa su. Na fi ɗaukar jigo a lokacin da na ci karo da faruwar wani al’amari da ya ɗaure min kai. Na kan tsaya in yi duba na tsanaki sannan in lalubo manufar faruwar al’amarin daga nan zan duba ta yadda idan saƙa zaren labarina zai yi hannun riga da wannan abu da ya faru kuma na gani domin ɓatar da sawuna gudun tuhumar na kwafi rayuwar wasu.
Ma fi yawan labarina gaskiya abu ne wanda ya faru a zahiri kuma na gani da idanuna.
Menene burinka a harkar rubutu?
Rai cike yake da buri, babu wani mai rai da zai bar duniya ba tare da buri ba.
Burina a harkar rubutu bai wuce Allah ya bani ikon in samar da wani littafi wanda za a dinga tunawa da ni ta dalilinsa ko bayan mutuwata kuma ya zama wannan littafin har a tsangayar ilimi za a iya nazartarsa.
Zuwa yanzu ya za ka iya bayyana nasarar da ka samu a harkar rubutu?
Nasarori kam Alhamdulillah! Domin, ko wannan hirar ma ai babbar nasara ce. Sannan na shiga gasanni mabambanta na fafata da manyan marubutan da idan a zahiri aka sanar da ni zan iya fafatawa da su ba zan yarda ba, kuma Alhamdulillah duk gasar da zan shiga ko da ban fito a sahun gwaraza ba, na kan fito a cikin ‘top’ 10 ɗin da aka zaɓa. Gare ni wannan babbar nasara ce sosai.
Sannan, silar rubutu na haɗu da mabambantan mutane waɗanda zumunci mai ƙarfi ya ƙullu a tsakanina da su har ta kai sukan ɗauki damuwata ta zama ta su. Babbar nasara ce wannan a rayuwa. Bugu da ƙari matata kafin mu yi aure bayan ta samu kwafin littafin da na wallafa ta dinga yawo da shi tsakanin ƙawayenta tana ɗaga ƙafa da bada labarin marubuci za ta aura, (dariya).
Har aka samu wata da ta fara neman ƙulla alaƙa da ni domin ta nuna nata ƙwazon a harkar rubutu. To kin san kishin mata, tuni ta bi ta toshe duk hanyar da wannan ƙawar tata za ta same ni. Nasara babba.
Wacce shawara za ka ba wa marubuta masu tasowa?
Shawarata ga marubuta masu tasowa bai wuce; su yi haƙuri su jajirce sannan duk abinda alƙalaminsu zai rubuta su tabbatar da ingancinsa domin shi kan shi rubutu wani makami ne mai dafi da za a iya amfani da shi a soki ahalin marubuci. Sannan a tsananta bincike akan dukkan jigon da aka ɗauka.
Ko kana da kiran da za ka yi ga manyan marubuta?
Kira na ga marubuta ne gabaɗaya yakamata su sani cewa; Idan kaine yau ba fa kaine gobe ba. Kuma a duk inda za a ambaci sunan wane ko wance ba karamin abun alfahari ne a ji wasu da suka fito daga wani ɓangare sun zo suna dukan kirji suna kirarin yadda ka/ki ka taimaka musu wajen cikar burinsu ba. Sannan, magana mai daɗi ita ma sadaka ce. Ko ba zaka taima ki mutum ba, ka/ki ba shi wasu mintoci ko da gaisuwarsa ne ka/ki amsa. Marubuta ‘yan’uwan juna ne ni ma shaida ne. Mu ƙara zage damtse wajen ƙarfafa zumuncinmu sannan duk inda aka samu mai burin ɗora alƙalaminsa akan takarda a taimake sa/ta da ‘yan shawarwari.
Mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.
