
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An samu ɓarkewar rikici a yammacin ranar Asabar yayin da ake tsaka da wasa bayan ƙungiyar Barau FC ta farke ƙwallon da Katsina United ta sha ta a filin wasan Dikko da ke garin Katsina.
An tsayar da wasan ne sakamakon raunata ɗan wasan Barau, Nana Abraham jim-kaɗan bayan ya farke ƙwallon, wanda hakan ya hefa ƴan wasa, jami’an wasa da magoya baya cikin firgici.
Tuni jami’an tsaro suka gaggauta shiga domin kwantar da hankali bayan alƙalin wasa ya tsayar da wasan, kana dafa bisani aka cigaba da bugawa.
Ana ganin al’amarin, wanda ya yi sanadin jefa tsoro da fargaba, ya nuna yadda rikici da kai ya kunno kai a wasannin ƙwallon ƙafa a Nijeriya bisa la’akari da gazawar kula da dandazon mutane.
Saidai, Ma’aikatar Ci-gaban Matasa da wasanni ta ƙaryata rahoton cewa an yi rikici yayin gudanar da wasan, tana mai kira ga jama’a dasu riƙa tantance labarai kafin amincewa da su, kamar yadda Rariya ta ruwaito.
