DAGA MUKHTAR YAKUBU
Fitaccen jarumi kuma shugaban hukumar fim ta ƙasa Ali Nuha ya nuna damuwar sa a game da ƙauracewa KILAF AWARD da ‘yan fim na Arewa musamman ‘yan Kannywood.
Ali Nuhu ,ya bayyana hakan ne a lokacin da yake wajen taron karrama jarumai na KILAF AWARD 2025 da aka yi a daren jiya Asabar 8 ga Nuwamba a ɗakin taro na gidan Gwamnatin Jihar Kano.
Tun da farko dai Ali Nuhu ya jinjinawa masu shirya taron ganin sun daɗe suna yi wanda har an zo karo na 8 in da yake cewa ” Dole ne a yi jinjina ga su waɗanda suke shirya shi wannan taron. Dalili kuwa shi ne shekaru takwas ana shirya taron, abu ne mai wahala. Ban san da wahala ba, sai lokacin da na zama shugaban hukumar finafinai ta ƙasa , kuma na ga mu ma idan za mu shirya namu na ga irin wahalar da muke sha”.
Dangane da maganar shigar da finafinai kuwa ya ce ” yana da muhimmanci mutanen mu musamman na Arewa wanda kusan KILAF AWARD shi ne taro da za su samu dama su kawo finafinan su. Don haka ya kamata a ce sun dage lallai su tsaya kai da ƙafa, don su ga sun shigar da finafinan su domin ya zama duk abin da ake yi su ma ya zama ana damawa da su.
Yin hakan shi ne zai sa a ƙara samun ci gaba da shi wannan taron. Sannan su ma finafinan namu da a ke so su ma a ga ana ganin su a duniya.
To wannan hanya ce za ta sa a rinƙa ganin su, domin su ma takwarorin su na duniya suna halartar taron.
Don haka ina kira a gare su da su rinƙa shigowa su ma ana damawa da su” . Inji Ali Nuhu.
