Nijeriya da Saudiyya sun ƙulla yarjejeniyar hajjin 2026

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta ƙulla yarjejeniyar gudanar da aikin Hajji ta shekarar 2026 da ƙasar Saudiyya yayin da ake gab da fara shirye-shiryensa.

An cimma haka ne a yayin wani biki a da aka gudanar a birnin Jeddah na Saudiyya.

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya sanya hannu a madadin Nijeriya, yayin da Mataimakin Ministan Hajji na Saudiyya, Abdulfatah Mashat ya wakilci ƙasa mai tsarki.

NAHCON ta bayyana cewa yarjejeniyar hujja ce akan cewa Nijeriya ta shiga jerin ƙasashen da za su gudanar da aikin ibadar a 2026.

Kawo yanzu babu tabbas game da adadin maniyyatan da za su je Saudiyya a bana, musamman saboda sanarwar NAHCON ɗin ta yi a watan Oktoba cewa hukumomin Saudiyya sun rage yawan kujerun Hajjin na Nijeriya daga 95,000 zuwa 66,000.

Kazalika, hukumar ta ce Saudiyya ta ɗauki matakin ne saboda Nijeriya ba ta cike dukkan guraben da aka ware mata a bara, inda aka samu giɓin alhazai 35,872, kamar BBC Hausa ta ruwaito.

By Babaji