
Ganin yadda Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ke ƙoƙarin haɓaka fannin lafiya, Asibitin Best Choice ya shirya duba nasu wasu nau’ukan cututtuka kyauta, inda ya yi rangwamen kaso 50 ga aikin tiyata.
Asibitin ya sake bijiro da wasu ayyukan jin ƙai a yunƙurinsa na cigaba da faranta wa al’umma kamar yadda ya saba lokaci bayan zuwa lokaci duba da yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf yake jajircewa wajen tallafa wa bangaren lafiya faɗin a jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa jagororin Best Choice za su duba masu waɗannan larurar kyauta, idan kuma abin ya kama za a yi aiki, za’a biya kaso 50, sannan a fara ganin likitoci daga ranar Alhamis, 13 ga Nuwamba 2025 zuwa zuwa Lahadi 16 watan a kyauta.
A sanarwar da hukumar gudanarwar Asibitin ta fitar, ta ce waɗanda aka tantance su kuma suke da buƙatar a yi musu aiki, za a yi musu ragin kaso 50 cikin 100 kan yadda ake biya kafin wannan damar.
Sannan za’a fara ganin marasa lafiyar ne tun daga ƙarfe 4 na yammacin kowace rana zuwa abinda ya sawwaƙa.
Ga jerin cututtukan da za a duba marasa lafiya akansu kamar haka:
Cutukan Hanci, Kunne Da Maƙogaro, akan ₦300,000 maimakon ₦600,000 kamar yadda ake biya a baya.
Cire ƙari (lipoma Excison) wato (Lipoma Removal) akan ₦100,000 maimakon 200,000
Aikin Ƙaba
Hernia Repair ₦200,000 maimakon 400,000
Tiyatar Cire Gwuiwa, wato Hydrocele Surgery akan ₦200,000 maimakon 400,000.
Tunda da farko da yake ganawa da Jaridar Alfijir labarai Shugaban asibitocin ƙwararru na Best Choice Kwamared Auwal Lawal Muhammad (Dan Malikin Garo), ya jaddada cewa suna gabatar da wadannan shirye shirye ne domin faranta wa al’umma tare da rage musu raɗaɗi na halin da suka tsinci kansu ciki.
Lawal ya kuma ci alwashin cigaba da bijiro da sabbin shirye shirye na kula da kiwon lafiya da ayyukan jin kai ta hanyar amfani da hanyoyin zamani don yin gogayya da sauran na duniya.
Kar ku manta wannan dama ta dan wani lokaci ce, kar ku sake a baku labari, wanda yaji zai iya sanarwa da wanda bai jiba
Asibitin Kwararru Na Best Choice yana nan a mazauninsa na dindindin dake Plot 782/783 tal’udu kusa da makarantar Sheikh Bashir Eli Rayya
Kazalika suna gudanar da ayyukan su ba dare ba rana tare da manyan ƙwararrun likitoci.
Za a iya tuntuɓar su ta yanar gizo [email protected]
Ko facebook Best Choice Specialist Hospital
Ko kira da whatsapp akan
+2347034951671
+234912 345 3534
+2342082443318
Mun zaɓi mu bada ire-iren waɗannan gudunmawar ne duba da yadda Mai girma Alh Abba Kabir Yusuf gwamnan jihar Kano yake bunƙasa harkar Lfy da sauran muhimman bangarori domin saukakawa al-umma musamman masu karamin karfi a dukkannin fadin jihar.

