Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana haka ta bakin Mataimakin Malam Faruk Lawal Joɓe, a lokacin da yake ƙaddamar da buɗe taron na ƙungiyoyin matasa.
Taron mai taken alfanu da matasa suka samu daga gwamnati da kuma hanyoyin da ya kamata subi wajen bayyana manufofin Gwamnatin domin cigaban al’umma.
Ma’aikatar matasa da wasannin da ofshin mai bai wa gwamna shawara akan harkokin matasa Dakta Abubakar Tsanni suka shirya taron.
Da yake gabatar da jawabin shi Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa” Gwamnatin Katsina, ta sake yin kyakkyawan shiri, wanda zai sake taimaka wa rayuwar matasa domin su dogara da kan su.
Gwamnan ya ƙara da cewa” tun zuwanmu bisa karagar mulki, muka yi abubuwa da dama, wanda suka taɓa rayuwar matasa, musamman yayan talakawa da mararsa galihu.
“Samar masu da guraben karatu a ƙasashen ketare, samar da ayyukan yi, samar da tallafi ga masu ƙananan sana’o’i a faɗin jihar Katsina da dai sauran su,”inji Dikko Raɗɗa.
Daga ƙarshe ya yi kira ga matasa da su ɗauki yin sana’a da mahinman ci, ya kuma yi kira a gare su dasu ɗauki abinda za’a gaya masu da muhimmanci.
Da yake jawabin maraba kwamishinan harkokin matasa da wasanniHon. Injiniya Surajo Yazeed Abukur ya yi godiya ga mahalarta taron tare da yin godiya ga Gwamna Malam Dikko Raɗɗa bisa kulawa da yake yi ga matasan.
Shima a nashi jawabin,mai ba gwamna shawara kan harkokin matasa Dakta Abubakar Tsanni ya bayyana cewa” natasa a jihar Katsina, a zuwan Malam Dikko Raɗɗa sun samu tagomashi da dama domin dogaro da kai.
Tsanni ya ƙara da cewa”Dukkan abinda su kai ma Gwamna Malam Dikko Raɗɗa indai na matasa ne, babu wanda ya tsallake yana badawa domin gina rayuwar matasa.
Daga ƙarshe ya ƙara yin godiya bisa yadda gwamnatin Jihar Katsina ta himmatu wajen taimaka wa matasa.
Taron wanda ya gudana a babban ɗakin taro na sakatariyar gwamnatin Jihar Katsina, ya samu halartar sakataren gwamnati jihar Barista Abdullahi Garba Faskari, wakilin Sarkin Katsina da sarkin Daura, Malamai masana, matasa maza da mata da sauran al’umma.
