Blueprint ta yi jimamin rasuwar ma’aikacinta, Yahaya Adamu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban rukunin kamfanin jaridar Blueprint, Mallam Salisu Umar, ya bayyana rashin Marigayi Yahaya Umar, wanda shi ne shugaban sashen wallafa na kamfanin, a matsayin babban giɓi ga kamfanin.

Salisu Umar, wanda ya ziyarci iyalan marigayin a Kaduna, ya bayyana kaɗuwarsa game da rasuwar Yahaya duba da kudancin alaƙarsu har a wajen aiki.

“Yahaya yana da ƙwazon aiki kuma ba ya wasa da aikin ofis. A kowane lokaci a shirye yake. Na rasa ginshiƙi”, inji shi, yana mai ƙarawa da cewa rashinsa babban al’amari ne ga tawagar ma’aikatan Blueprint.

Ya kuma yi masa addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa tare da sanya shi a Aljannar Firdausi.

A safiyar ranar Asabar ne Yahaya Adamu ya rasu a Kaduna bayan fama da wani gajeren rashin lafiya.

Haka kuma daga cikin mahalarta ta’aziyyar marigayin akwai Daraktan jaridar Blueprint, Alhaji Ibrahim Sheme.

A wata sanarwa da Shugaban sashen kula da ma’aikatan kamfanin, Nuhu Sani ya fitar, ya ce an gudanar da jana’izar marigayin ne a yankin Gundumar Kabala Costain a jihar, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Marigayin ya rayu da mata ɗaya da ƴaƴa goma.

By Babaji