Sanusi kaɗai muka sani a matsayin Sarkin Kano — Kwankwaso

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sake jaddada cewa Muhammadu Sanusi II shi ne kaɗai Sarkin Kano da aka amince da shi, yana mai cewa duk wasu da aka naɗa “daga Abuja ” ba su da wata karɓuwa a idon Kanawa.

Kwankwaso ya yi wannan batu ne a yayin bikin yaye ɗalibai karo huɗu da Jami’ar Skyline University of Nijeriya ta gudanar a Kano ranar Asabar, inda ya ce gwamnatin jihar da al’ummar Kano sun amince da Sanusi shi kaɗai Sarki, sauran kuma “masu ikirari ne kawai”.

Ya yaba da ci gaban da jami’ar ke samu tare da dagewarta wajen inganta ilimi, yana mai bayyana farin cikinsa da ganin cewa mata sun fi rinjaye a cikin waɗanda suka kammala karatu sama da kashi 60%. Ya shawarci maza da su tashi tsaye wajen karatu domin kada mata su ci gaba da ba su tazara.

“Sanusi shi ne kaɗai sarkin da Kano da gwamnati suka amince da shi,” in ji Kwankwaso.

Da ya juya ga batun tsaro kuwa, Kwankwaso ya nuna damuwa kan ƙaruwa da rashin tsaro a Arewa, yana gargaɗi cewa ƴan ta’adda na ƙoƙarin kutsawa Kano ta hanyar kananan hukumomi da ke iyaka da wasu jihohi, kamar Tsanyawa, Shanono, Gwarzo da Karaye.

Ya roƙi Shugaba Bola Tinubu ya ɗauki matakin gaggawa, yana mai cewa gazawar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyi na nuna raunin jagoranci ne.

“Idan gwamnati ta kasa kare rayuka da dukiyoyi, to dole ta koma ta sake tunani,” in ji shi.

Kazalika, yana mai cewa matsalar tsaron ta fara ne daga Zamfara yanzu ta yaɗu zuwa Sokoto, Kebbi, Kaduna har ta fara barazanar zuwa Kano da Jigawa.

Tsohon gwamnan ya tuna da muhimman matakan tsaro da gwamnatinsa ta ɗauka a lokacin da yake mulki, yana kira ga gwamnatin tarayya ta ƙara dagewa wajen kare ƴan ƙasa.

A nasa jawabin, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, wanda shi ne babban shugaba, wato (Chancellor) na Skyline University, ya shawarci sabbin ɗaliban da aka yaye da su rungumi gaskiya, ƙirƙira da hidimar al’umma, yana mai cewa ilimi ba shi da amfani idan bai amfanar da jama’a ba.

“Ilmi ba tare da aiki ba kamar fitila ce babu mai ko kananzir, tana da haske a ƙa’ida amma marar amfani cikin duhu,” in ji Sanusi.

Sannan ya yaba da ci gaban jami’ar ta ke samu, da kuma yawan mata a cikin waɗanda suka kammala karatu, yana mai fatan hakan zai ƙara ƙarfafa wa mata guiwa wajen shiga harkokin gwamnati da sauran muhimman sassa na ƙasar.

By ukarofi