Gwamnatin Katsina ta buƙaci Sheikh Masussuka ya bayyana gaban kwamitin malamai

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da shirya zama tsakanin fitaccen malamin nan Sheikh Yahya Masussuka da kwamitinin malaman jihar domin ya kare kansa.

Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta ce ta buƙaci malamin ya bayyana a gaban kwamitin malaman jihar domin kare kansa game da wasu kalaman da yake furtawa a karatunsa.

Tun da farko wasu malamai a jihar ne suka shigar da ƙorafinsu ga gwamnatin jihar saboda zarginsa da wuce gona da iri a karatuttukansa.

Bayan ƙorafin malaman sai wasu malaman da ke goyon bayansa suka shigar da ƙorafinsu gaban gwamnati cewa wasu na yi wa Sheikh Masussuka barazana da cin mutuncinsa, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

Sanarwar ta ce bayan zaman da za a yi tsakanin malamin da kwamitin malaman jihar za a samar da wasu ƙa’idojin wa’azi a jihar.

Inda gwamnatin ta ce za ta tabbatar an bi ƙa’idojin da aka cimma tare da hukunta duk wanda ya kauce musu.

By ukarofi