Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Wata gobara ta tashi a daren Talata zuwa safiyar Laraba a kasuwar tsofaffin ƙarafa da katako da ke Gombe, inda ta ƙone shaguna fiye da 30 tare da lalata dukiya mai darajar miliyoyin naira.
Shugaban ƙaramar hukumar Gombe, Barista Sani A.A. Haruna, ya ziyarci wurin tun lokacin da wutar ke ci, inda ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga al’umma.
Ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa, tare da tabbatar musu da cewa hukumar ƙaramar hukumar za ta ci gaba da tallafa musu.
Haruna ya kuma yaba wa mazauna unguwannin da ke kusa da kasuwar bisa taimakon da suka bayar wajen hana ɓarna da kuma kare kayan mutane daga shiga hannun ɓarayi.
Ɗaya daga cikin waɗanda gobarar ta fi shafa, Alhaji Abdullahi A.A. Laja, shugaban ƙungiyar masu tsofaffin ƙarafa na jihar ya ce gobarar ta tashi ne daren Talata kuma ta bazu da sauri, inda ta laƙume shaguna da dama nasa.
Ya zargi cibiyoyin kashe gobara da jinkiri, suna cewa ba su da ruwa, yayin da na jami’ar Gombe suka nemi izini kafin su fito.
A cewarsa, lamarin ya yi kamari har sai da shugaban ƙaramar hukumar ya iso wurin.
Laja ya ce shagunan da suka kone sun ƙunshi katako, tsofaffin karafa, kayan gine-gine da na’urori.
Duk da asarar, ya gode wa shugaban kan taimakon gaggawa da ya kai.
