Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kuɗin shekara ta 2026 mai nauyin N1,368,127,929,271 ga Majalisar Dokokin Jihar Kano, inda ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kammala muhimman ayyuka da kuma zurfafa ci gaban da ya shafi kowa a faɗin jihar.
Gwamna ya bayyana cewa gwamnatin sa ta cimma fiye da kashi 80 cikin 100 na alƙawuran da ta yi a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, gwamnan, ya ce kasafin ya ƙunshi kaso 68% na kashe-kuɗi (capital expenditure) wanda ya kai N934.6 biliyan, da 32% na kuɗin gudanarwa (recurrent expenditure) wanda ya kai N433.4 biliyan — ɗaya daga cikin kaso mafi girma na zuba jari kan gine-gine a tarihin jihar kwanan nan.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa rabon kasafin ya bi diddigin manyan muradun raya jihar, inda Ilimi ya samu kaso mafi girma N405.3 biliyan (30%), ayyukan gine-gine suka biyo baya da N346.2 biliyan (25%), sannan lafiya ta samu N212.2 biliyan (16%).
“Waɗannan abubuwan sun nuna ƙudurorinmu na zuba jari sosai a fannin raya ɗan Adam, kare lafiyar jama’a, da shimfiɗa tubalin ci gaba mai ɗorewa,” in ji gwamnan.
Ya ce ɓangarorin tattalin arziki da walwalar jama’a suna da matuƙar muhimmanci a cikin kasafin 2026, inda noma, tsaro, kasuwanci, ruwa, muhalli, yawon buɗe ido, ci gaban mata da matasa, da mutanen da ke da buƙatu na musamman suka samu ingantaccen tanadi.
Kazalika, gwamna Yusuf ya ƙara jaddada ƙudirin gwamnati na daidaita kasafin da muradun jama’a, yana mai cewa kasafin kuɗin ya kasance “tsarin aiki na gaskiya kuma na bayyana, wanda aka yi don tabbatar da ingantacciyar makoma ga Kano.”
Daga nan gwamna ya roƙi ƴan majalisa da su sahale cikin gaggawa, yana mai jaddada cewa rawar da suke takawa wajen sa ido da tattaunawa mai muhimmanci wajen mai da kasafin wani aiki da zai shafi rayuwar jama’a kai tsaye.
