Fasaha ta kawar da zamanin sojan gonar ƙuri’a, inji Shugaban INEC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) ya ce samar da na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’a ta BVAS ya taimaka wajen daƙile ayyukan sojan gona a yayin zaɓukan Nijeriya.

Amupitan ya bayyana haka ne yayin taron ‘Digital Nigeria International Conference and Exhibitions’ a Abuja, wanda aka yi a ranar Talata, 11 ga watan Nuwamba ƙarƙashin jagorancin Hukumar kula da Ci-gaba Fasahar Labarai ta ƙasa (NITDA).

Shugaban na INEC, wanda Misis May Agbamuche-Mbu, kwamishina ta ƙasa ta wakilce shi, ya ce zamanin yin zaɓe sama da ɗaya ga mutum da yaudara ya wuce a sakamakon samar da BVAS.

Ya bada misali da zaɓen da aka yi a Anambara, wanda ya samu agajin BVAS wajen tantance masu zaɓe, abinda ya sa aka samu sahihin sakamakon zaɓen, wanda ya taimaka aka shigar da na kaso 99 a shafin sakamako na IReV tun a ranar zaɓen daga dukkan rumfunan jihar.

Ya bayyana cewa, zaɓukan da aka yi a baya a Nijeriya sun fuskanci matsalolin rashin ingancin kayayyakin fasaha, wanda hakan ya sa aka yi ta samun nakasu daga ɓangaren hukumar wajen aiwatar da ayyukanta.

A cewar farfesan, an yi nasarar daƙile ayyukan sojan gona da kaɗa ƙuri’a sama da sau guda ga mutum ɗaya a sanadiyyar samuwar BVAS, wanda hakan abu ne da zai inganta hanyoyin samar da sahihan sakamakon zaɓuka a ƙasar.

By Babaji