Kano: Ƙaramar Hukumar Bichi ta dakatar da ayyukan dillancin filaye don inganta tsaro

Spread the love

Majalisar Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano, ta haramta wa dillalan filaye da gidaje marasa rijista cigaba da gudanar da harkokin dillanci a faɗin yankin.

Sakataren Mulki, Hon. Anas Muhammad da ya wakilci shugaban karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ne ya bayyana haka a wani zama da karamar hukumar ta yi da masu riƙe da sarautu da dillalan domin inganta tsaro a faɗin yankin.

Ya ce, hakan na da manufar yaki da kawar da gurbatattun dillalai da baragurbin mahukunta dake saba doka a yayin saye da sayarwa na, filaye, gidaje da ba da haya ga bakin da ba a tantance su bisa ka’ida ba, wanda hakan ke janyo matsala da barazana ga rayuwar jama’a baki daya.

“Gwamna ya yi doka na hana sayarwa ko yanka wuri ko bayarwa wsnda za a yi amfani da shi idan ba ya shafi aikin gwamnati ba, duk wanda ya zo ya ce gwamnati ta ba shi wuri kaza ko zai sayar ko wani abu ya sanya ku a ciki to kar ku shiga wannan al’amarin.”

Wakili Abbas Idris Bayero da ya wakilci Hakimin yankin, Alhaji Mannir Sanusi, ya shawarci dillalan bai wa karamar hukuma hadin kai domin tsaftace sana’arsu da tabbatar da zaman lafiya da tsaro cikin aminci, sannan ya sake jan hankalin dagatai, masu unguwanni da kuma dillalan cewa laifi ne ajiye baƙo ba tare da an sanar da hukuma ba.

“Idan ba a ssnar da mai unguwa ba, aka tabbatar cewa ba a sanar ba ai shi ya fita, amma kai ba za ka fita ba.”

Malam Nasiru Ibrahim, wakilin Dagacin Bichi, ya yi ƙarin haske game da rashin bin ƙa’idar sana’ar kasa bisa bincike; dillalai marasa kungiya ne tushen bayar da gidaje ga wasu baki baragurbi, da kuma gudun biyan kudi 5 0/0 da ake bayarwa kafin saka hannu a takardar ciniki a hukumance, bisa haka dillalai masu kungiya suka dau aniyar, muddin suka samu hadin kan masu unguwanni wajen tantance musu dillalan garuruwansu, za su yi wa wadanda aka yarda da su rijista domin kawar da wannan matsala.

“Akwai dagatai a nan wadanda za su tabbatar da sadda muka je wajensu muka zauna da su suka hada mu da dillalan dake garuruwansu, kuma har yanzu muna tafiya da su, amma akwai inda har yau ko dillali daya ba a kawo ba kuma ana cinikin gona ana komai.”

Masu ruwa da tsaki kan zaman lafiyar al’uma: wakilin DPO, Abdul Dansarai ya ce a kiyaye harkokin dillancin bisa doka da oda, yayin da wakilin DSS, Martins Ambrose ya ja hankalin kungiyar dillalai a kan lura da dabi’un dillalai kafin a yi musu rijista, kuma da zarar an ga bakin haure da ba a san asalinsu ba a yi gaggawar sanar da su.

Akan haka ne Kwamandan Hisba na yankin, Malam Murtala Safiyanu ya yi nasiha kada la’ada ta zama la’ana a ji tsoron Allah wajen kiyaye gaskiya da amana domin bunkasa zaman lafiya da kuma arziƙin yankin.

By Babaji