Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta tabbatar da tuhume-tuhumen ta’addanci akan Nnamdi Kanu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta tabbatar da aikata laifukan ta’addanci akan tsararren jagoran ƙungiyar ƴan fafatukar kafa ƙasar Biafara (IPOB), Nnamdi Kanu, wanda aka shigar da tuhume-tuhumensu akansa a gabanta.

Da yake gabatar da hukunci akan shari’ar, Alƙali James Omotosho ya tabbatar da tuhuma guda uku da masu ƙara suka shigar akan Kanu tun farkon lokacin da aka maka shi a kotu.

Ya ce, barazanar tashin-tashina da Kanu ya yi a wani faifan bidiyo ya haddasa fargaba da shiga ƙunci ga al’umma a yankin Kudu maso Gabas, lamarin da ya ƙarfafa zarge-zargen da ake masa.

Alƙalin ya bayyana cewa, bisa la’akari da hujjar da ɓangaren da ke tuhumar ya gabatar, alamun ta’addanci sun bayyana akan Kanu sakamakon manufarsa da ayyukansa.

Mai Shari’ar ya ƙara da cewa, jagoran na IPOB ya ƙi amfani da damar da aka ba shi na ya gabatar da hujjarsa da ke nuna ba shi da hannu a laifukan, amma ya ƙi yin hakan.

A yanzu haka kotun tana alƙalanci akan laifuka guda bakwai da ake tuhumar Kanu a kansu.

By Babaji