CITAD ta ƙaddamar da sabuwar manhajar ‘Reportrix’ don sa ido a wasu laifuka

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma (CITAD) ta ƙaddamar da wata manhaja mai suna Reportrix, da zai tattara rahotanni da bayar da rahoton cin zarafin mata (GBV), yaɗa labarun ƙarya, take haƙƙin faɗin albarkacin baki da kuma lura da ayyukan gwamnati da aka fara ba a gama ba.

An ƙaddamar da manhajar ne a taron manema labarai da aka gudanar a ofishin CITAD na Kano, a ranar Laraba.

Daraktan CITAD, YZ Ya’u, ya ce rarraba ayyukan dandalan na waɗannan rahotonin cibiyar ya sa mutane da dama ke fuskantar ƙalubale wajen samun damar amfani da su.

Inda ya ce ya bayyana cewa Reportrix ta zo da sauƙakaƙiyar hanyar bayar da rahoto cikin dandali guda, wanda hakan zai ƙarfafa gaskiya da riƙon amana tare da tallafa wa aikin fafutuka a faɗin ƙasar nan.

Manhajar na ɗauke da manyan sassa huɗu: tashar sirrin bayar da rahoton cin zarafin mata (GBV), aikin bayar da rahoton ƙarya tare da samun bayanan bincike (fact-check), na’urar bibiyar take haƙƙin sadarwa da kuma dandali na bayar da rahoton lura da ayyukan gwamnati ko aikin da aka fara ba a gama ba, ko aiki mara inganci.

Masu amfani da manhajar za su iya tura hotuna, abun da ake zargi, wurin da abin ya faru, da bayanin abin da ya faru, tare da samun ilimi don fahimtar kafafen yaɗa labarai, adalci ga jinsi, da tsaro a yanar gizo.

Wannan manhajar ta Reportrix ta ƙunshi mafarin bayanai (dashboards), taswira, harsuna daban-daban, sanarwar gaggawa, da ƙarin matakan tsaro da kariyar bayanai. A cewar CITAD, dandalin zai taimaka wajen samar da ingantattun bayanai don tattaunawar manufofi tare da bai wa ƴan ƙasa damar shiga cikin harkokin mulki.

Kazalika Ya’u ya yi kira ga jama’a da su sauke manhajar, sannan ya buƙaci hukumomin gwamnati, ƙungiyoyin farar hula, da ƙungiyoyin cigaban al’umma, da su yi haɗin gwiwa wajen magance irin wannan abubuwa da ake bayar da rahotonsu. Ya kuma yi kira ga kafafen watsa labarai da su faɗaɗa yaɗa wannan sabon aiki domin a samu wayar da kai yadda ya kamata a cikin al’umma.

By ukarofi