Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Yayin da wasu masu boye sunayanensu kamar yanda mu ka sha yin bayani a baya da yin shigar-burtu da nuna su Hausawa ne; ke ci gaba da zama a boye ba sunan gaskiya ba hoto; sun maida hankali sosai wajen asalin zargin kwangilar da a ka ba su ta aibata kiran Shehu Mujaddadi na ISTIƙAAMA don hakan ya hana biris da addini samun gindin zama a Arewacin Nijeriya. Ban yi mamaki ba sam da taron da a ka gudanar a London na neman lallai sai an murde wuyan tarihi an juya kiran da Shehu Mujaddadi ya yi zuwa hoton da wasu daga yammawan duniya ke mannawa Musulmi na bakin fentin ta’addanci. Da zarar yammawa na son muzanta musulmi don kai mu su farmaki sai su laƙaba mu su suna irin “fanatics, islamists, eɗtremists” da sauran kalmomi na zayyana Musulunci da zama addini na rashin nishaɗi ko shan romon duniya, kwankwadar barasa da yawon ta zubar. Na fahimci hatta Sir Ahmadu Bello da Sir Abubakar Tafawa Balewa da su ka yi jagoranci zamanin ‘yancin Nijeriya a jamhuriya ta farko sun zauna ne da yammawan nan dutse hannun riga. Rawani da su ke sakawa ko rike tasbaha a London na konawa yammawa rai don haka na Faransa ma ba su yi wata-wata ba su ka marawa Ojukwu baya da ya ayyana ɓallewa daga Nijeriya bayan juyin mulkin 1966 da a ka shekar da jinin su Firimiya da kuma abun da ya biyo baya na yaƙin basasa.
Jama’a hoton kwangilar da a ka ba wa ‘yan bazata Hausawan shigar burtu na soshiyal midiya ya fito? Za ku ƙara tabbatar da haka ta yadda ‘yan iƙirarin kafa Hausa zalla su ke marawa ‘yan awaren Biyafara baya da zafafawa lallai sai an saki Nnamdi Kanu duk da ya na kotu don fuskantar tuhumar haddasa kisan gilla ga ɗimbin jami’an tsaro, fararen hula na Arewa akasari Hausawa. Yaya mai ikirarin yaƙi da ‘yan ta’adda zai buƙaci a saki ɗan ta’adda da tuni an gurfanar da shi gaban kotu? Makirci ya fito fili duk mai nazari ya gane. Tabbas mutanen nan ba Hausawa ba ne kuma sun karɓi kwangilar nan da ƙarfin gaske don ra’ayinsu ne ci gaba da kushe Hausawa da kullum a ke ganinsu da masu nacewa kan bautar Allah maɗaukakin Sarki. Me hujjar kashe matafiya daga Zaria da su ka je Filato ɗaurin aure watannin baya? Me dalilin kashe ‘yan tawagar da su ka ziyarci Shehu Dahiru Bauchi a shekarun baya? Me dalilin kashe irin su Janar Alkali da jefa motar sa ruwa? Masu irin wannan muguwar dabi’ar ce za su tsere Washington su na fesa gubar a na yi wa wasu kisan ƙare dangi? A nan zan maimaita abun da na rubuta a baya cewa akwai ‘yan yankin Kaduna ta kudu da wasu daga Binuwai gidan Bishop Wilfred da ke cewa da zarar ‘yan Biyafara sun ɓalle za su yi mu su mubaya’a su hade da su. Hakan tamkar cimma muradin Gideon Orkar ne da ya yi wuf zai yi wa Janar Babangida kisan gilla don kafa ƙasar ‘yan aware amma haka ba ta tadda ruwa ba.
A nan duk wanda ku ka gani ya na alaƙanta rashin tsaro na Arewa maso yamma da Shehu Mujaddadi to hakika ɗan kwangila ne kuma ba mai ƙaunar addini ba ne. Masu basaja da ke cikin kwangilar ba Hausawa ba ne duk da su kan yi magana da harshen Hausa amma rashin adalcinsu ne yarensu da addininsu.
Duk wani ɗan kwangila da ya yi mu su to ya fito da sunansa na hakika da hotonsa da kuma kauyensu a Arewa. Idan hotonsu ya saba da wannan rubutun na wa sai a yi alƙalanci. Shin akwai wanda zai yi ta maza duk da matsorata ne ya fito don a yi muhawarar keke da keke da shi? Don haka duk wanda ya cigaba da buya a ramin kura ku yi watsi da shi yaron mai son tada husuma ne Ouba Ali Mohaman ne na Kamaru kuma tabbas duk dubunsu zai cika za a cafke su don fuskantar tuhumar cin amanar ƙasa da ta’addanci.
Gaskiyar magana duk wannan fitinar ba za ta hana musulunci ko kiristanci a Arewa ba. Buƙatar mu duk wanda zai yi wata da’awa ya fito fili kawai a san shi ko waye ne kamar yanda wasu Kiristoci su ka buɗe shafi na kiristocin Arewacin Najeriya masoya Pastor Azzaman Azzaman. Shin ba mu haska alaƙar ‘yan kwangila da Azzaman ba?.
Manufar wannan sako shi ne tantance barcin makaho da kuma saukakawa ‘yan iƙirarin Hausa zalla su amsa wannan kalubale don gane matsayinsu. Mun buƙaci su fito da hotonsu da sunansu na asali amma sun ƙi yin hakan bayan buƙata ta fiye da mako daya. Yanzu ga wannan hanya musamman wadanda a cikinsu ke nacewa cewa ba wanda ya isa ya kore su daga musulunci ai ba mai wuta ba mai aljannah a cikin mu. Mutanen nan kan tsaya a kwarin kunya ba tare da ayyana addinin da su ke bi ba. An samu ɗaya daga cikinsu wanda har ya taba yin basaja da zayyana mai dauke da sunan Manzon Allah amma ya fito ƙarara ya yi yekuwa ya ce shi mai bin tsarin gargajiya ne. Akwai wadanda in mun matsa lamba sai su cika rigarsu da iska ko su cillo hoton ‘yan ta’addan daji a matsayin neman shashantar da tuhumar da a ke yi mu su. Mutanen nan kan zundumawa Shehu Mujaddadi zagi na rashin albarka amma sai su dawo yabawa Nnamdi Kanu da ya ingiza a ka zubar da jinin ‘yan Arewa, su na masu zayyana shi a matsayin dan gwagwarmayar kwatar ‘yanci da kira da kakkausar murya cewa gwamnati ta sake shi. Mu na jiran kalmar shahada daga mutanen nan don shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, Annabi Muhammadu Manzon Allah ne. In kuma ba musulmi ba ne, su yi shahada irin ta addininsu.
Abu na biyu mun yi imani kwangila mutanen nan su ka karbo inda su kuma ke cewa mu na lankaya mu su abun da ba haka ba ne. Don Allah su barranta kan su da wannan addu’ar ta Allah ya hallaka su indai su ‘yan kwangila ne.
Kun ga a nan da shahada da addu’a ba sa buƙatar sai sun fito da hotonsu da sunansu na gaskiya.
Gaskiyar magana akwai sauki har kullum ka san da wa ka ke muhawara ko jayayya. Da dai za a bar ‘yan ikirarin Hausa zalla wato ‘yan kwangilar rusa Arewa, za su cigaba da zayyana kan su a matsayin Hausawa kuma har ma masu kwatar ‘yancin Hausawa. Tubka da warwara da shirga karya hatta daga manyansu, sun sa tababar sahihancin da’awar mutanen nan. Salon rubutu da zagin Shehu Usmanu Mujaddadi da mafi miyagun kalmomi duk na nuna ayar tambaya kan iƙirarin ‘yan kwangilar. Sam Hausawa ba sa zagin Shehu. Hasalima ma dabi’ar Hausawa ce girmama Mujaddadi da amfana daga littattafansa. Don haka ba raba daya biyu matuƙar ka ga wani na zagin Mujaddadi to wa imma ba Bahaushe ba ne ko addini ba layinsa ba ne.
Maiwada Danjuma Yahaya na daga misalan ‘yan kwangila masu ikirarin Hausa zalla daga jihar Nasarawa kuma bayanasa sun nuna shi ɗan ƙabilar Alago ne. In za a tuna a shekarun baya an samu wani jagoran tsangayar kabilar Eggon a jihar Nasarawa Baba Alakyo da ya jagoranci jama’arsa su ka kirkiro tafiyar OMBATSE wato lokaci ya yi na ‘yan Eggon su karɓi madafun ikon jihar Nasarawa. Hakika jarrabawar ta haddasa rasa rayuka musamman na jami’an tsaro. Arangama da ‘yan sara-suka na Ombatse a shekara ta 2013 ta yi sanadiyyar kisan ‘yan sanda 74 da jami’an tsaron farin kaya 10. Jami’an tsaro sun gaza samun galaba a lokacin kan Ombatse don hasashen karfin tsafin Baba Alakyo da ya ba wa dakarunsa wani ruwan haɗi su ka kwankwada. Yau ga wani da ya zaɓi harshen Eggon da karawa da Hausa ya fito ya yi wuf ya tsunduma cikin ruruta fitinar ƙabilanci a Arewa.
Bincike na nuna ɗaya daga gaggan jagororin ‘yan kwangilar nan ma dan ƙabilar Ibo ne da a ka haifa a Arewa don haka ya na iya tankwara harshe ya yi magana da Hausa. Wani lokacin har karambanin jan ayar Alkur’ani ya ke yi da yin fassarar gatari. Hakanan akwai ma ayar tambaya kan wani daga jihar Adamawa da ke iƙirarin Bagobiri ne amma tocila ta haska BWATIYE ne wato kabilar Bachama da ke da yawan jama’a a Numan. Yo ai akwai wanda mu ka haska da tabbas Bafulatani ne amma ya ke shigar-burtu a ikirarin karya na Hausa zalla. Na ga ya cika rigarsa da iska.
KAMMALAWA
Abu ne mai muhimmanci mu ci gaba da haska wadannan mutane don a fahimci inda su ka dosa wato haddasa yaƙi tsakanin musulmi a yi ta dauki ba dadi daga masallatai ta zugar wai a daina bin limamin wata ƙabila sallah ko a bijirewa wanda ya fadi abun da ya sabawa muradun ‘yan kwangila. Abun ban haushin ‘yan kwangilar ba su da asara don ba masallaci su ke zuwa ba balle annamimancin na su ya rutsa da su. Ba su da ko bishiyar barankaci a arewacin Arewa ko kufayin kakanninsu. Don haka su ke ta ruruta fitinar nan ba dare ba rana. Ina yi mu su mugun albishir cewa yakin nan da su ke muradi ba za a yi ba, sai kaka?. Kazalika ko ‘yan kwangila su tuba ko su fada komar jami’an tsaro don fuskantar tuhumar ta’addanci da cin amanar kasa.
A nan ina yabawa wata ƙungiyar mabiya addinin Kirista. masoya Pastor Azzaman da su ka fito fili su ka bude shafi ba tare da yin basaja ba. Saura kaɗan ma na ce ‘yan kwangilar ƙaryar Hausa zalla ne. Gaskiya na yaba mu su yadda su ka bayyana ko su waye ne.
Zan rufe da jinjinawa ƙarin jama’a masu kishin Arewa da na ke gani su na watsi da farafagandar ‘yan kwangila. Masha Allah mu na ƙara godiya ga Allah don yanzu ‘yan kwangila ba sa samun fagen yin daɗala ba tare da fuskantar masu wancakali da ƙarerayinsu ba.
