Nan ba da jimawa ba za a sako ƴan makarantar Neja da aka sace, inji Shugaban APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawa Yiltwatda ya ce nan ba da jimawa ba za a sako ɗalibai da malaman makarantar St. Mary’s Catholic Primary and Secondary School, Papiri da ke Ƙaramar Hukumar Agwara a Jihar Neja da aka yi awon-gaba da su a ranar Juma’ar da ta gabata.

Yiltwatda ya bada tabbacin hakan ne a lokacin da ya jagoranci kwamitin ayyukan (NWC) jam’iyyar zuwa ziyarar ƙarfafa gwiwa ga Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) reshen jihar Neja a jiya Laraba.

Ya ce, APC tana tare da iyalan waɗanda abin ya shafa, al’ummar Kiristoci da gwamnati a yayin da suke alhinin al’amarin.

“Mun zo nan ne domin miƙa saƙon taya jajenmu game da abin takaicin al’amarin garkuwa da ya faru a jihar”, inji Yiltwatda.

“Zukatanmu suna tare da ku, addu’o’inmu na tare da ku, kuma yaran nan za su dawo cikin iyalansu nan ba na daɗewa ba”, inji Shugaban APCn.

Ya ƙara da cewa, duk da fargaba akan al’amarin, akwai tsammanin ceto su duba da yadda ake cigaba da gudanar da addu’o’in mataki na ƙasa aka gano su cikin aminci.

Da fari, Yiltwatda ya ziyarci Gwamna Umaru Bago a gidan Gwamnatin jihar, inda ya samu ba’asi akan ƙoƙarin gwamnati da hukumomin tsaro wajen ceto mutanen.

Kazalika, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa matakan da ya ɗauka zuwa yanzu, yana mai cewa tuni suka fara fitar da sakamako mai kyau.

A ƙarshe, ya yi addu’ar fatan ceto ɗalibai da malaman nan ba da jimawa ba domin su koma cikin iyalansu.

By Babaji