Majalisar ƙaramar hukumar Bichi ta saka ɗambar gina wa dagatan yankin 44 zaunanniyar fada ƙarƙashin sahalewar Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ne ya bayyana haka, a yayin hirarsu da jami’ar yaɗa labaran yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo a ofishinsa, jim kaɗan bayan ganawarsa da dagatai goma da aikin zai fara ta kansu.
Da yake jawabi shugaban ƙaramar hukumar, ya ce, alƙawari ne da suka ɗauka za su cika na gina wa dukkan dagatan ƙaramar hukumar Bichi sabuwar fada, sakamakon rashin gyara na tsawon lokaci.
Kazalika da sanin cewa dagatai iyayen ƙasa ne mafi kusa da jama’a da suke taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwar zamantakewar al’uma, ta fuskar samar da zaman lafiya da tsaro kasancewarsu masu faɗa a ji a dukkan yankunansu.
Fadodin da aka ɗauka na farko sun haɗa da: Yola, Doddo, Fagolo, Damarga, Danzabuwa, Waire, Kaukau, Huggalawa, Tinki da kuma Tukwibi.
“Waɗannan su ne dagatan da Allah ya sa cikin ikonsa aikin zai fara ta kansu, ko da wane lokaci yanzu za mu je mu fara wannan aiki, ɗan kwangila ya zo, mai girma Gwamna ya ba mu dama mu je a fara, shi ne dalilin da muka zauna da su yau, mu ka ce su je su yi shiri za mu turo musu ɗan kwangila domin ya zo su ba shi wuri ya fara.”
Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya ja hankalin takwarorinsa ciyamomin Kano cewa; su daure su gudanar da irin wannan aiki a ƙananan hukumominsu, domin hakan zai ƙara dankon alaƙa da haɗin gwiwar kyautata al’amuran jama’a a tsakaninsu, inda kuma ya yi kira ga dagatan su ma, su alkinta fadodin idan an yi, ta fuskar kula, tattali, tsafa da makamantansu.
“Yana ɗaya daga cikin abin da ya sa muka zauna da su, za a inganta fada sosai yadda za ta zauna, duk bakon da za su yi in Allah ya yarda ba za su ji kunya ba, za a fitar da fasali mai kyau yadda kowa in ya zo ya gani za ki ga an ɗauka a jihar Kano baki ɗaya in sha Allahu.”
Dagacin Waire, Alhaji Mustapha Halilu Danwaire da dagacin Fagolo, Malam Habibu Adamu sun yi farin ciki da godiya a madadin kafatanin dagatan ƙaramar hukumar bisa wannan tagomashin alheri da ba su yi zato ba kuma ya same su.
“Kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi; mun tabbata mai girma ciyaman yana da kishin gidaje irin namu na gargajiya.”
“Saboda haka muna masa godiya, ya zo da wani abu wanda yake ba a taɓa zuwa da shi ba a wannan ƙaramar hukuma kai a Kano baki ɗaya ma, don haka muna masa fatan alheri, Allah ya sa ya gama lafiya, Allah ya yi jagora. Muna kuma godiya ga mai girma Gwamna game da jajircewar da yake yi a kan harkokin da suka shafi ilimi da sauran aikace-aikace, muna godiya.”
