Ƙungiyar ba da agajin gaggawa ta (Red Cross) Reshen Jihar Kano ta kammala bita na tsawon kwana uku a ƙaramar hukumar Bichi.
Sakataren kungiyar, Alhaji Musa B. Abdullahi, ya ce, an shirya bitar ne domin koya wa ‘yan kungiyar (Red Cross) dake ƙaramar hukumar dabarun yadda za su iya ba da agajin gaggawa a lokacin da aka samu wani iftila’i.
Ya bayyana cewa wannan shiri wani bangare ne na shirin, da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa ke tallafa wa ƙungiyar (Red cross) da shi, wanda ya shafi kananan hukumomi uku, Bichi, Karaye, da Kumbotso, inda ya ce, a halin yanzu ƙungiyar ta kammala ayyukan bitar a ƙananan hukumomin Kumbotso da Bichi.
“Mun yi musu gwaji da aka yi hatsarin mota da mashin waɗansu suka ji rauni; suka zo suka ba su gudunmawar agajin gaggawa. Sannan kuma ga kayan aiki da muka zo muka ba su waɗanda za su riƙa yin amfani da su, a kowane lokaci idan ana yin taro; a masallatai ne, makarantu ne, taron iyayen yara ne da ake yi a makarantu da sauransu, ko kuma a unguwanni.”
Alhaji Musa Abdullahi ya ƙara da cewa matasan, ‘yan ƙungiyar (Red Cross) sun nuna fahimintar wasu game da bitar, musamman inda suka nuna irin ƙwarewar da za su iya wajen ba da agajin gaggawa a lokutan iftila’In gobara da haɗurra na mota ko rushewar gine-gine, da nutsewa a ruwa.
Ya lura cewa masu shirya bitar sun nuna gamsuwa da ƙwarewa da jajircewarsu.
Haka kuma, ya yaba da ‘yan (Red Cross) na Bichi saboda kasancewarsu masu jajircewa da aiki tuƙuru, inda ya ƙara da cewa suna haɗuwa a kowane mako domin duba da inganta shirin bayar da agajin gaggawa.
“Idan har aka yi wa mutum wannan horon da aka yi mana a harka ta ba da agajin gaggawa irin wannan, to ba wai iya ƙaramar hukumar Bichi ko Kano ko Nijeriya ba, duk duniya inda ka je da wannan satifiket din, dole za a saurare ka kuma za a ba ka dama ka gudanar da ba da agaji a ko’ina ne kuma kowane irin iftila’i ne ya afku.” Garba Abdulkadir, shugaban ƙungiyar agajin gaggawa reshen Bichi.
Alhaji Musa Abdullahi ya kuma yi godiya ga majalisar ƙaramar hukumar Bichi saboda goyon bayanta, wanda ya ba su damar amfani da kayan aikin majalisar wajen gudanar da bita da raba kayan agajin gaggawa.
“Shi ne ya sa muka ga cewar Bichi tana ɗaya daga cikin garin da yakamata su mori wannan dama da muke da ita. Kuma Alhamdulillahi muna samun gudunmawa da fahimta a ɓangaren karamar hukuma, ga shi ma har sun ba su ofis kamar yadda dama muke buƙata domin su dinga haɗuwa a ofis wajen bita tare da ba su kayan aikin agaji.”
