Kwamitin kyautata alaƙa tsakanin ‘yan sanda da jama’a sun gana a Bichi

Spread the love

Kwamitin Kyautata alaƙa tsakamin ‘yan Sanda da jama’ar gari, (PCRC) na ƙaramar hukumar Bichi sun yi kira ga shugabannin kasuwar Bichi su ci gaba riƙe gaskiya da amana a mu’amalarsu, musamman a cikin kasuwancinsu.

Shugaban Kwamitin, Alhaji Ali Ibrahim ne ya yi kira lokacin da suka kai ziyara ofishin shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwar ta Bichi.

A yayin ziyarar, kwamitin na (PCRC) ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ali Ibrahim sun yi nasiha da jan hankali ga shugabannin kasuwar a kan su ci gaba da haƙuri da juriya da yin aiki tuƙuru domin cigaban al’uma. Sun yi alkawarin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙungiyar domin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyar al’uma a kasuwar baki ɗaya.

A nasa ɓangaren shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwa ta (Bichi Traders Multi Purpose Cooperative Society limited), Alhaji Abubakar Mazahim Saleh, ya yi farin ciki sakamakon yadda kwamitin na (PCRC) suka kawo musu ziyara, bayan takardar da ƙungiyar ‘yan kasuwar suka aika wa kwamitin tun a watan da ya gabata dangane da neman zama da kwamitin.

A wani cigaban kuma, ƙungiyar ‘yan kasuwa ta (Bichi Traders Multi-Purpose Cooperative Soceity Limited) ta karɓi makamanciyar wannan ziyarar daga shugaban ƙungiyar fitilar jama’ar Bichi, Alhaji Lurwanu Idris Malikawa, inda shugaban ƙungiyar kasuwar, ya nuna jin daɗi da yaba wa bisa wannan ziyara.

Da yake jawabi, shugaban ƙungiyar ta Fitilar Jama’ar Bichi, Alhaji Lurwanu Idris Malikawa-Garu, ya bayyana jin daɗin sa game da irin tarbar da ƙungiyar ‘yan kasuwar suka yi musu, inda suka samu damar tattauna muhimman batutuwa da suka shafi cigaban kasuwar da haɓaka tattalin arziki da kasuwanci a ƙaramar hukumar.

Alhaji Lurwanu Malikawa-Garu ya yi kira ga ƙungiyar da ta dage wajen haɗa kan ‘yan kasuwa tare da wayar da kan sauran ‘yan kasuwar ƙauyuka, a kan muhimmancin kasuwar tare da ci gaba da amfani da kafafan yaɗa labarai wajen wayar da kan al’uma, a kan abin da ya shafi kasuwar da kasuwanci baki daya.

By ukarofi