Kamfanin Paystack ya kori Ezra Olubi bisa zargin ɓata suna

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin fasahar kuɗi na Nijeriya, Paystack, wanda kamfanin Stripe ke da shi, ya sallami ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa kamfanin, Ezra Olubi, bisa hujjar jawo wa kamfanin mummunar illa ga suna da martabarsa sakamakon wasu tsoffin saƙonni da aka tono daga shafinsa na sada zumunta.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar, Paystack ya bayyana cewa matakin da ya ɗauka ba ya da alaƙa da binciken cin zarafin aiki da ake ci gaba da yi a kansa ta hannun wani lauya mai zaman kansa.

Ya ce, ya yi amfani da haƙƙinsa na doka kamar yadda ke cikin kwangilar aiki, tare da tabbatar da cewa an bi dukkan matakan aiki da kuma biyan dukkan haƙƙoƙinsa na kuɗi yadda ya dace.

A cewar kamfanin, “A matsayinmu na kamfani da ke ƙarƙashin doka, dole ne mu ɗauki mataki cikin gaggawa idan wani hali zai iya lalata amincewa da mu. Bayan nazari, mun yi amfani da haƙƙin da kwangilar aikinsa ta ba mu domin kawo ƙarshen aikinsa.”

Paystack ya kuma bayyana cewa binciken da ake yi kan zargin cin zarafin aiki na ci gaba da tafiya ƙarƙashin jagorancin kamfanin lauyoyi Aluko & Oyebode, yana mai jaddada cewa binciken da korar nasa abubuwa ne biyu daban.

Kamfanin ya ƙara da cewa, cibiyoyin kuɗi na fuskantar babbar barazanar suna da martaba, domin amincewar jama’a da na hukumomin sa ido su ne ginshiƙin aikinsu. Don haka, duk wani al’amari da zai iya girgiza wannan amincewa kan tilasta wa kamfani ɗaukar mataki cikin hanzari.

A matsayin misali, kamfanin ya ambaci murabus ɗin wuri na tsohon Shugaban Bankin Absa, Arrie Rautenbach, wanda ya sauka daga muƙaminsa bisa zargin rashin ɗabi’a, a matsayin misalin yadda manyan cibiyoyi ke gaggauta kare ƙa’idojin shugabanci.

A baya, Olubi ya wallafa wani rubutu inda ya ce lauyoyinsa suna duba sahihancin sallamar tasa domin a ga ko ta yi daidai da manufofin cikin gida na kamfanin.

Ya nace cewa ce-ce-kucen da aka tayar kan tsoffin saƙonninsa ba su wakilci halinsa a aikace ba.

Wata majiyar da ta yi magana da TechCabal ta ce martanin da Olubi ya yi kan batun tsoffin saƙonnin ya haifar da shakku kan ƙarfin gwiwarsa na ci gaba da riƙe matsayi na jagoranci a irin wannan lokaci da ake cikin matsin lambar jama’a da na hukumomin sa ido. 

Majiyar ta ƙara da cewa Olubi ya raina girman lamarin, abin da ya sa kamfanin ya ɗauki matakin kare sunansa da martabarsa.

Sallamar ta Olubi ta sake buɗe muhawara kan rikici tsakanin kare suna, bin ƙa’idojin aiki, da kuma ɗaukar alhaki ga waɗanda suka kafa kamfani, lamarin da ke nuna wani muhimmin sauyi a tarihin Paystack yayin da yake ƙoƙarin ƙetare wannan jarrabawa ta fuskar jama’a da hukumomi.

By ukarofi