Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD
Ambaton ayoyin Bible da Mai shari’a James Omotosho ya yi yayin yanke hukuncin zaman-ɗauri ga jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya janyo muhawara mai zafi a faɗin ƙasar game da matsayin addini a tsarin shari’ar Nijeriya mai bin tsarin dimokuraɗiyya na zamani.
A ranar 20 ga Nuwamba ne Mai shari’a Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ya same shi da laifi a tuhume-tuhume bakwai na ta’addanci, inda ya yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.
Kotun ta ce, Kanu ya yi amfani da shirye-shiryen wajen tayar da hankula, kai hari kan jami’an tsaro, lalata dukiyoyin jama’a da kuma barazanar kai wa ofisoshin diflomasiyya hari.
Alƙalin ya jaddada cewa Nijeriya ba za ta taɓa rarrabuwa ba, yana mai cewa neman cin gashin kai ba zai taba halatta ta hanyar tashin hankali ba.
Ya kuma bayar da umarnin kwace na’urorin Kanu tare da a tsare shi a wajen da babu damar amfani da na’urorin zamani.
Sai dai abin da ya fi jawo ce-ce-ku-ce shi ne bayanin da Mai shari’a Omotosho ya yi cewa hukuncin da ya dace da laifukan da aka same shi da su shi ne kisa, amma ya sassauta hukuncin ne saboda koyarwar addini kan jinƙai.
“Kotun na nuna masa jinƙai ne saboda koyarwar Annabi Isa Almasihu kan jinƙai. Kanu bai nuna nadama ba; yana girman kai da taurin kai. Duk da haka, zan daidaita adalci da jinƙai,” inji alƙalin.
Daga nan ya ambaci aya daga littafin Bible, babi na 23, a matsayin hujjar ƙarfafa matsayin jinƙai.
Wannan ambato ya raba ra’ayin ‘yan Nijeriya gida biyu. Wasu sun yi tambaya ko hakan ya dace da ƙasar da kundin tsarinta ya ayyana a matsayin mai bin tsarin shari’a na boko, ba na addini ba.
Misbahu El-Hamza ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa ya yi mamakin yadda alƙalin ke ta ambaton Littafin Bible a hukuncin da ya kamata ya kasance bisa tanadin doka kaɗai.
Haka zalika, Bolarinwa Oladeinde ya yi tambaya kan ko ambaton littafin addini wani ɓangare ne na tsarin shari’a.
Sai dai wasu sun kare alƙalin, suna masu cewa zancen bai wuce ƙarin haske na ɗabi’a ba.
Fatima Abdulhadi Zubairu ta ce a ganinta ba wani abin damuwa ba ne, ganin cewa alƙalin Kirista ne, wanda ake yanke wa hukunci Kirista ne, kuma mafi yawan mabiyansa ma Kiristoci ne.
A gefe guda kuma, Isah Ogedengbe Abu Khuzaimah ya zargi masu sukar alƙalin da nuna ɓangaranci. Ya ce da a ce alƙalin Musulmi ne ya ambaci Alƙur’ani, da tuni an cika kafafen sadarwa da zargin “Musuluntar da shari’a”.
