Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon lauyan jagoran haramtacciyar ƙungiyar Biyafara ta IPOB, Aloy Ejimakor, ya ce duk yawan lauyoyin da za a tara a gaban kotu ba zai sauya hukuncin da aka yanke wa Nnamdi Kanu ba kan laifin ta’addanci.
Ejimakor ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels a shirin The Morning Brief, inda ya ƙaryata ra’ayin da ke cewa idan an samu ƙarin lauyoyi masu ƙarfi, da an iya sauya sakamakon shari’ar.
A cewarsa, “Ba na ganin ko da lauyoyi miliyan ɗaya sun tsaya a bayan Nnamdi Kanu, hakan zai canja hukuncin da aka yanke. Abin da ya faru ya riga ya faru.”
Ya ce, duk da girmama ikon kotu, bai gamsu da hukuncin ba, yana mai jaddada cewa shaidun da aka gabatar ba su tabbatar da alaƙa kai tsaye tsakanin jawabai ko watsa shirye-shiryen Kanu da rikicin da ya yi sanadin mutuwar jama’a a yankin Kudu maso Gabashin ƙasar nan ba.
“Na ƙi amincewa da hukuncin, da tuhumar, da kuma yanke hukuncin da aka yi,” inji shi. “Amma mai yiwuwa alƙalin ya ga shaidun sun wadatar a ganinsa. Ni kaina ban ga wata hujja bayyananniya da ke nuna cewa watsa shirye-shiryen nasa ne suka haddasa tashin hankalin ba. Har yanzu ma ana ci gaba da tashin hankali; shin har yanzu wancan watsa shirye-shiryen ne ke haddasa shi?”
Ejimakor ya yi kwatancen shari’ar da wasu shari’o’in tarihi da suka shafi manyan mutane, inda ya ce an yanke hukunci a kansu ne tun kafin a kammala tsarin shari’a yadda ya kamata. Ya kwatanta shari’ar da abin da ya faru a zamanin Annabi Isa a gaban Pontius Pilate, inda ya ce “tun da farko mutane sun riga sun yanke shawarar abin da suke so, ba su tsaya sauraren shari’a ba.”
Ya kuma ambaci shari’ar Nelson Mandela, inda ya ce duk da cewa ba a kama shi da makami ba, an yanke masa hukunci ne saboda ana kallon tasirinsa a matsayin barazana. Haka kuma ya yi ishara da shari’ar Obafemi Awolowo a shekarun 1960, inda aka tuhume shi da yunƙurin kifar da gwamnati duk da kasancewarsa farar hula.
A cewarsa, “Ba na cewa alƙalin ya nuna wariya ba, amma a bayyane yake tsarin ya ɗauki alƙawarin sai an ga an yanke wa Kanu hukunci tun daga ranar da aka kama shi a Kenya.”
A ranar Alhamis da ta gabata ne alƙalin kotun tarayya Justice James Omotosho ya yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai da rai kan tuhume-tuhume guda bakwai na ta’addanci. Alƙalin ya ce watsa shirye-shiryen da Kanu ke yi sun tayar da hare-hare kan jami’an tsaro, lalata muhimman kadarorin gwamnati, tare da barazana ga ofisoshin jakadanci.
Alƙalin ya jaddada cewa Nijeriya ƙasa ce guda ɗaya da ba a iya raba ta ba, yana mai cewa neman ‘yancin kai ta hanyar tashin hankali ba za ta taɓa halatta ba. Haka kuma ya bayar da umarnin a kwace na’urorin watsa shirye-shiryen Kanu tare da a tsare shi a wani wuri mai tsaro ba tare da damar amfani da na’urorin sadarwa na zamani ba.
Lauyoyin Kanu sun bayyana hukuncin a matsayin mai tsanani fiye da kima, suna mai cewa za su ɗaukaka ƙara. Ejimakor ya kuma tabbatar da cewa an mayar da Kanu zuwa gidan yari na Sokoto Custodial Centre, yana mai sukar matakin da cewa ya nesanta shi da iyalansa da kuma lauyoyinsa.
An fara kama Kanu ne a shekarar 2015, daga bisani ya tsere bayan samamen sojoji a gidansa a 2017, kafin a sake kama shi a Kenya a shekarar 2021 a cikin yanayi da ya jawo ce-ce-ku-ce a fagen shari’a da siyasa.
