NDLEA ta fatattaki manyan ƙungiyoyin safarar ƙwayoyi da kama ɗimbin ƙwayoyi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta ƙaddamar da gagarumar samame a faɗin Nijeriya, lamarin da ya kai ga rushe aƙalla ƙungiyoyi shida da ke jagorantar safarar miyagun ƙwayoyi, da cafke tan-tan na kayan maye, tare da damƙe manyan shugabanninsu tara.

Wannan samame ya zo ne a daidai lokacin da shugaban hukumar, Birgediya Janar Muhammad Buba Marwa (mai ritaya), ya bayyana cewa suna shiga “farmaki marar sassauci” gabannin lokacin bukukuwa — wani lokaci da masu aikata laifi ke amfani da cinkoso da zirga-zirgar jama’a wajen safarar kayan maye.

Daraktan Yaɗa Labarai na NDLEA, Femi Babafemi, ya ce waɗannan ayyuka da aka gudanar a makon sun shafi jihohi da dama, ciki har da aikin da ya gano wata babbar hanyar safarar kwayar methamphetamine daga Afirka ta Kudu zuwa Onitsha.

Ya bayyana cewa, jami’an NDLEA sun damƙe Ebulue Lotanwa Uzochukwu mai shekara 30 da Christopher Michael Ndibuisi, wanda ya dawo daga Afirka ta Kudu, bayan sun zo karɓar kwantena da ke ɗauke da 5.40kg na methamphetamine da 10.70kg na loud (wani irin ƙwayar taba mai ƙarfi), da wasu ƙwayoyi daban-daban da aka ɓoye cikin bututu da aka shigo da su ta filin jirgin sama na MMIA da ke Legas.

A wani samame a MMIA, jami’an hukumar sun gano kwantena da ake shirin tura wa Gabon, inda aka gano 2.30kg na cocaine da aka ɓoye cikin sassan motoci, ciki har da “brake serɓo”.

Bincike ya kai ga kama Ameh Solomon, dillalin jigilar kaya, wanda bayan tambayoyi ya tona asirin wani dillalin sassan mota, Nwafor Tochukwu Boniface, wanda aka damƙe a Kasuwar Duniya ta Legas.

Haka nan, a jihar Kogi, an cafke tirela ɗauke da 4,700kg na kwayar skunk a Kabba, tare da kama mutane uku da ke rakiya. Bincike ya kai ga kama babban mai kayan — Marcus Danladi Dan Mangu — a garin Jos, bayan aikin sirri.

Irin waɗannan kame na NDLEA na nuna yadda ƙungiyoyin safarar ƙwayoyi ke ci gaba da ƙirƙirar dabarun ɓoye kaya.

Wannan salo na nuna irin ƙalubalen da hukumomi ke fuskanta — musamman a lokacin bukukuwa — lokacin da masu safara ke ƙaruwa saboda yawan shiga-da-fita da kuma kasuwanci.

By ukarofi