
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya bayyana kaɗuwarsa bisa rashin fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma jagoran Ɗarikar Tijjaniya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, wanda a ya rasu a ranar Laraba.
Gwamnan a wata takarda daga mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Isma’ila Uba Misilli, ranar Alhamis, ya bayyana marigayin shehin malamin a matsayin magabaci na daban, wanda rayuwa da karantarwarsa ta yi tasiri akan miliyoyin al’umma.
Ya ce, marigayin ya sadaukar da kansa wajen yaɗa addinin Musulunci musamman duba da yadda ya shahara da karantar da Alƙur’ani mai girma, hadisi da fiƙihu a bisa fahimtar sufanci.
Shugaban gwamnonin ya ƙara da cewa marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen abinda ya shafi zaman lafiya, haɗin kai, juriya da tarbiyyar addini.
Kazalika, gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsu ga iyalana mamacin da ƴan Tijjaniya gami da ɗaukacin al’ummar Musulmi baki ɗaya.
Ya kuma yi masa addu’ar Allah ya jiƙan sa ya gafarta masa kurakuransa da sanya a Aljannar Firdausi.
