El-Rufa’i ya koma ADC a hukumance

Spread the love

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya koma jam’iyyar ADC a hukumance ta hanyar ansar katin jam’iyyar.

Nasir El-Rufai ya fice daga jam’iyyar APC ne jim kaɗan bayan baban zaɓe na ƙasa na shekarar 2023, inda ya koma jam’iyyar SDP, wanda daga bisani kuma ya fice daga jam’iyyar.

A yanzu a iya cewa sun haɗe da tsohon mataimakin ƙasa kuma kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar PDP, wato Alhaji Atiku Abubakar.

Komawar El-Rufai ADC a hukumance wani mataki ne da ake ganin zai kawo sabon salo a siyasar adawa wajen ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a Zaɓen 2027.

A wannan Alhamis ɗin ce El-Rufai ya kammala rajistar zama mamba na jam’iyyar ADC a mazaɓarsa ta Unguwar Sarki da ke birnin Kaduna, inda ya yi alƙawarin amfani da jam’iyyar ADC wajen fuskantar abin da ya kira rashin ƙwarewa a jagorancin gwamnatin jihar.

By Babaji