Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da aikin titin filin Polo

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Aikin titin wanda zai fashi daga Filin Polo- zuwa Ring Road da nisan kilomita huɗu a birnin Katsina.

Wannan aikin na daga cikin shirin gyaran birni na gwamnatin jihar (Katsina Urban Renewal), wanda aka tsara domin inganta zirga-zirgar ababen hawa, bunƙasa haɗin kai tsakanin wurare da kuma ƙarfafa harkokin kasuwanci a cikin birnin.

Kwamishinan ayyuka, Injiniya Sani Magaji Ingawa, ya bayyana cewa titin zai zama muhimmiyar hanyar da za ta haɗa manyan tituna, wanda zai saukaka sufuri da kasuwanci cikin birnin.

Dan majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina Hon Aliyu Albaba ya nuna godiya ga Gwamna Raɗɗa kan fifita ayyukan inganta birni, tare da jaddada fa’idodin aikin wajen rage matsalar tsaro da bunƙasa harkokin kasuwanci a cikin birnin Katsina.

Shugabannin ƙaramar hukumar Katsina, Hon Isa Miqdad AD Saude ya yaba da aikin, yana mai jaddada cewa zai jawo zuba jari, samar da ayyukan yi da ƙarfafa tattalin arzikin birni. Sannan ya bayyana cewa mutanen ƙaramar hukumar za su cigaba da bada goyon baya ga gwamnati don cigaba da ire-iren waɗannan ayyukan.

Wakilin yan kwangila ya tabbatar da cewa za a gudanar da aikin bisa ƙa’idojin da aka gindaya kuma cikin wata 12 kamar yadda aka tsara.

Da yake ƙaddamar da aikin titin Gwamna Raɗɗa ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na sauya Katsina zuwa birni na zamani da ingantaccen tattalin arziki ta hanyar ayyukan raya birane da ƙauyuka, inda ya bayyana cewa wannan aikin titin wata shaida ce ta jajircewar gwamnatin sa wajen inganta ababen more rayuwa da ci gaban jama’a.

By ukarofi