Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta amince da wani gagarumin tallafi na yuro biliyan 15.5 domin tallafa wa yaƙin neman zartar da sabbin ayyukan makamashi mai ɗorewa a nahiyar Afrika, wani yunƙuri da ake sa ran zai inganta samar da wutar lantarki ga miliyoyin jama’a tare da ƙarfafa ci gaban tattalin arzikin ƙasashe masu tasowa.
Wannan shiri, wanda Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula ɓon der Leyen, da Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, suke jagoranta, na da nufin ƙara samar da makamashi tsaf, faɗaɗa hanyoyin samun wuta ga al’umma, da kuma haɓaka jarin da zai taimaka wa ci gaban dogon lokaci a nahiyar.
A wata sanarwa da Ofishin Jakadancin EU a Nijeriya da ECOWAS ya fitar a Abuja, an bayyana cewa EU ce ta ja ragamar tara kuɗaɗen, inda ta fito da fiye da Euro biliyan 15.1 kaɗai — ciki har da fiye da Euro biliyan 10 da Shugabar EC, ɓon der Leyen, ta yi wa “Team Europe” a madadin ƙasashen mambobi da cibiyoyin kuɗin su.
Ta ce, “A yau duniya ta nuna ƙawancen ta da Afrika. Tare da yuro biliyan 15.5, mun ƙara kuzari ga sauyin makamashi a nahiyar. Miliyoyin mutane za su iya samun wutar lantarki—wuta ta gaskiya da za ta sauya rayuwar iyalai, kasuwanci da al’ummomi gaba ɗaya.”
Shirin ya haɗa da muhimman ayyukan Global Gateway da za su samu haɗin gwiwar Jamus, Faransa, Denmark, Italiya, Netherlands da Spain, tare da gudunmawar European Inɓestment Bank (yuro biliyan 2.1) da European Bank for Reconstruction and Deɓelopment (Euro miliyan 740).
Haka kuma, Italiya ta ƙara da Euro biliyan 2.4, Jamus fiye da yuro biliyan 2, Netherlands (ciki har da FMO) yuro miliyan 250, Portugal Euro miliyan 113, Denmark yuro miliyan 81, Sweden yuro miliyan 44, Austria yuro miliyan 5, yayin da Ireland ta bada yuro miliyan 5.
A ɓangaren Afrika, Babban Bankin Ci Gaban Afrika (AfDB) ya yi alƙawarin ware aƙalla kashi 20 cikin ɗari na Asusun Ci Gaban Afrika karo na 17 domin zuba jari a makamashi mai sabuntawa. Norway ma ta ce za ta bayar da yuro miliyan 53 a cikin gudunmawar da ta tanada tsakanin 2026–2028.
A cewar masu shirya yaƙin neman sa hannun duniya, waɗannan kuɗaɗen za su taimaka wajen samar da gigawatt 26.8 na sabbin hanyoyin samar da wutar lantarki mai tsabta, tare da bai wa aƙalla gidaje miliyan 17.5 damar samun ingantacciyar wuta.
