
Tsohon Shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya bayyana cewa abin da ya faru a Guinea-Bissau ba juyin mulki ba ne duk da cewa ya janyo ruɗani da tashin hankali a fadin ƙasar.
Jonathan ya ce, al’amarin ya taɓa shi matuƙa fiye da ranar da ya kira marigayi Muhammadu Buhari domin taya shi murnar nasarar zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2015.
Tsohon shugaban ƙasar ya kasance a Guinea-Bissau ne a lokacin a matsayin shugaban tawagar West African Elders Forum da ke sa ido kan zabukan kasar, lokacin da aka ruwaito juyin mulki. Saboda fargabar tsaro da tashin hankali, daga baya ya bar kasar ta hanyar wani jirgin saman Ivory Coast.
A wata hira da ya yi da Symfoni a ranar Juma’a, Jonathan ya ce abin da ya faru ba juyin mulki ba ne, yana mai kiran shi “ceremonial coup”.
Ya bayyana cewa, lamarin ya tada masa hankali saboda ya saba da yadda ake gudanar da juyin mulki a nahiyar, kuma yadda aka gabatar da batun ya saba al’ada.
Ya kuma nemi ƙungiyoyin AU da ECOWAS da su bayyana sakamakon zaɓen domin tabbatar wa al’ummar haƙiƙanin wanda ya yi nasara.
Jonathan ya jaddada cewa babu wanda ya kama Shugaba Embaló, kuma abin da ya faru bai kamata ya dakatar da bayyana sakamakon zaɓen ba.
