Rashin tsaro: ‘Yan Nijeriya na da ƴancin neman ɗauki daga ƙasashen waje, inji Obasanjo

Spread the love

Tsohon Shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo ya ce ƴan Nijeriya suna da cikakken ƴancin neman taimakon ƙasashen waje idan gwamnatin ƙasar ta gaza kare rayukansu.

Obasanjo ya yi jawabin ne a wani taron Kirsimeti a Jos, inda ya ce bai kamata a ji kunyar neman taimako ba idan gwamnati ta kasa cika babban nauyinta na tsaro.

Tashar talabijin ta Channels ta ruwaito cewa Obasanjo ya ce a zamanin da ake amfani da tauraron ɗan-adam da jiragen sintiri, bai kamata ƴan ta’adda su riƙa kashe mutane su bace ba.

Ya zargi gwamnati da gazawa, inda ya ce hare-hare da kashe-kashe sun yi yawa, kuma ’yan kasa sun gaji da zubar da jini.

Kazalika, ya tunatar da sace ’yan matan Chibok, yana mai cewa matsalar tsaro tana taɓarɓarewa maimakon ta inganta

Haka kuma ya jaddada cewa kariyar ’yan ƙasa ita ce aikin farko na kowace gwamnati, amma a halin yanzu gwamnati ba ta iya kare al’umma yadda ya kamata.

Tsohon shugaban ƙasar ya yi kuma yi tir da masu ƙoƙarin mayar da kashe-kashe batun addini ko ƙabila, yana mai cewa “dukkanmu ’yan Nijeriya ne, kuma ana kashe mu ba tare da bambanci ba”, lamarin da ke ƙara haddasa koma-baya ga harkokin ci-gaban ƙasar.

By Babaji